✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wataqila Morata ya koma Ingila

Rahotanni sun nuna xan qwallon gaba a kulob xin Real Madrid na Sifen Alvaro Morata ya fara tunanin komawa Ingila da qwallo ganin yadda ba…

Rahotanni sun nuna xan qwallon gaba a kulob xin Real Madrid na Sifen Alvaro Morata ya fara tunanin komawa Ingila da qwallo ganin yadda ba ya samun damar yin wasa a kan kari a kulob xin Madrid na Sifen.
Alvaro Morata wanda kulob xin Madrid ya sayo daga kulob xin Juventus na Italiya a bara kawo yanzu ya buga wasanni bakwai ne kacal a gasar La-Liga ta Sifen inda ya zura qwallaye 8.
Hakan ta sa xan qwallon mai kimanin shekara 24 ya fara tunanin canza sheqa a qarshen kakar wasa ta bana kuma tuni kocin kulob xin Chelsea na Ingila Antonio Conte ya fara yunqurin saye xan qwallon.