✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Watan azumi muke, a guji caca — Naira Marley

Ya kamata a koma ga Allah ko don watan Azumi.

Shahararren mawakin nan na Najeriya, Azeez Adeshina Fashola da aka fi sani da Naira Marley ya yi gargadi ga masu yin cacar da ake kira ‘bet’ ko ta Baba Ijebu da su farga cewa a watan azumi ake, su yi watsi da cacar su koma ga Allah.

Naira Marley ya fadi haka ne a ranar Alhamis 1 ga Ramadan, inda ya rubuta gargadin a shafinsa na Twitter yana cewa, “’yan uwana a addinin Musulunci, ya kamata ku farga ku yi watsi da caca, kuma ku koma ga Allah ku yi azumi.”

Haka washegari Juma’a ya yi wani rubutun jan hankali a shafinsa na Twitter inda ya ce, a watan azumi ne Allah Madaukaki Ya saukar da Alkur’ani Mai girma domin ya zama kariya da shiriya ga talikai, inda ya kawo surar Alkur’ani ta 2 aya ta 185.

Gargadin shahararren mawakin ga ’yan caca bai zo wa mutane da mamaki ba, lura da yadda cacar bet ko ta Baba Ijebu ta zamo ruwan dare a jihohi Kudu maso Yamma, ta yadda baya ga matasa hatta magidanta maza da mata da tsofaffi na yin cacar, yayin da wasu magidanta ke tura ’ya’yansu wasu kuma matansu suke ba kudi su je su yi cacar.

A farkon makon jiya ma wakilin Aminiya a Legas ya yi kicibis da wata tsohuwa tukuf, wadda da fari ya dauka bara take domin da kyar take tafiya sai ya ga ta tattaka ta karasa teburin mai cacar Baba Ijebu, ta je aka ba ta lamba ta buga.

Wannan na nuna cewa, mawaki Naira Marley ya lura da yadda jama’ar yankin suka mai da hankali kan cacar ce, don haka ya yi gargadi gare su, ya kuma yi masu tuni cewa a watan azumi muke a yanzu.