✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Watakila FC Barcelona ta koma Gasar Firimiyar Ingila

Rahotannin da ke fitowa daga Sifen sun nuna akwai yiwuwar kulob din FC Barcelona ya koma buga gasar rukuni-rukuni ta Ingila da aka fi sani…

Rahotannin da ke fitowa daga Sifen sun nuna akwai yiwuwar kulob din FC Barcelona ya koma buga gasar rukuni-rukuni ta Ingila da aka fi sani da Fimiriya ko kuma Gasar rukunin Faransa da aka fi sani da Ligue 1 idan yunkurin da yankin Cataloniya yake yi na samun ’yancin kai ya tabbata.

Shugaban kulob din Barcelona Joseph Maria Bartomeu ne ya bayyana haka a ranar Lahadin da ta wuce a lokacin da yake amsa tambayoyin ’yan jarida.

Shugaban ya ce ganin yadda ala’amarin neman ’yancin kai da ’yan Yankin Cataloniya suke yi yana kara zafafa idan hakarsu ta cimma ruwa, ko shakka babu kulob din FC Barcelona zai tattara nasa-ya-nasa ya koma Ingila ko Faransa don ci gaba da buga gasar rukuni-rukuni a daya daga cikin kasashen Ingila ko Faransa, saboda yanzu haka kulob din yana zaune ne a yankin Cataloniya na Sifen, idan kuma aka ba ’yan Cataloniya ’yanci to tilas kulob din ya canza matsuguni.

A ranar Asabar da ta wuce kulob din Barcelona ya buga wasansa da na Las Palmas a filin wasa na Nou Camp ne ba tare da ’yan kallo ba, inda mahukunta kulob din suka bayar da umarnin rufe filin wasan saboda yamutsin da ke faruwa a tsakanin ’yan sanda da kuma masu fafutukar samun ’yancin kai na Cataloniya al’amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu, sannan da dama suka jikkata. 

Sai dai rahotanni sun nuna da wuya burin masu yunkurin samun ’yancin Cataloniya ya tabbata, don sun sha yin irin wannan yunkuri a baya amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba.