✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata ta kai mijinta kotu saboda yana sa ta yin sallah da jinin al’ada

Wata matar aure a Garin Gwagwa da ke Abuja ta maka mijinta a kotu kan zargin tilasta mata kwanciyar aure da kuma yin ibadar salla…

Wata matar aure a Garin Gwagwa da ke Abuja ta maka mijinta a kotu kan zargin tilasta mata kwanciyar aure da kuma yin ibadar salla a lokacin da take fuskantar jinin al’ada.

Matar wadda Allah Ya albarkace su da ’ya daya a aurensu na shekara 3, ta bukaci babban kotun lardi na Birnin tarayya da ke Garin Jiwa Abuja ta shigar da karar a ranar Litinin da ta gabata, da ta raba auren nasu.

Alkalin kotun mai shari’a Muhammad B. Marafa, ya nemi sanin hujjar wanda ake karar kan dalilinsa na tirsasawa matarsa bukatar, kamar yadda ta yi zargi bayan ya ankarar da shi cewa, hakan ya saba da karantarwan alqur’ani mai girma da kuma koyarwan Manzon Allah S.AW da ke cikin hadisi.