✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata sabuwa ga `yan Arewa:-Rijistar sabuwar jam`iyyar PDM

A ranar Juma`ar makon jiya Sakatariyar Hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC, Uwargida A. C. Ogakwu ta bada wata sanarwa a Abuja, inda take…

A ranar Juma`ar makon jiya Sakatariyar Hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC, Uwargida A. C. Ogakwu ta bada wata sanarwa a Abuja, inda take shelar amincewar Hukumarsu na yi wa wasu sababbin jam`iyyun siyasa guda biyu rijista. Sabbin jam`iyyun sune Jam`iyyar Independent  Democrats wato ID da kuma jam`iyyar People`s Democratic Mobement, rijistar da Sakatariyar ta ce ta samu ne bisa ga tanade-tanaden tsarin mulkin kasar nan na shekarar 1999, da akai ma kwaskwarima da kuma tahade-tanaden dokokinn Hukumar zaben na shekarar 2010.
 Makalar tawa ta yau zata mayar da hankali ne akan rikidewar da PDM wadda `yan siyasar dake da ra`ayin tafiyar siyasar marigayi Janar Shehu Musa`Yar`aduwa suke wa lakabi da Fadama, ita ce  kungiyar siyasar da marigayi Janar Shehu Yar`aduwan ya kirkiro ya kuma tafiyar da kudaden aljihunsa, sannan ya yi amfami da ita ya shiga rushashshiyar jam`iyyar SDP a zamanin jamhuriya ta uku ta mulkin tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida da bata kai labari ba (1991 zuwa 1993). Mai karatu, ya kamata in maka matashiya, akan waccan kungiyar siyasa ta PDM, kungiyar da zakaranta ya yi cara a wancan lokacin, ya kuma ci gaba da cara har a cikin wannan jamhuriya ta hudu a dukkan fadin kasar nan. Tun a wancan karon Janar Shehu ’Yar`aduwa, ya kai ga samun nasarar neman tsayawa rushashshiyar jam`iyyar SPD takarar nemn shugabancin kasar nan, bayan zaden fidda gwanin jam`iyyar ya fitar da shi.
 Bisa ga irin wannan nasara da marigayi Janar `Yar`aduwa ya samu a inuwar jam`iyyar SPD, alhali `yan takara daga sassa daban-daban na kasar nan sun shiga wancan zabe, amma dai marigayi Shehu `Yar`aduwa ya yi nasara akansu, ba ma wai a kasa baki daya ba kawai, a`a, har ma a jihohinsu na asali.
daya daga cikin wadanda Janar Shehu `Yar`aduwa ya yi nasara akan su a jiharsa shine Alhaji Latef Jakande, tsohon Gwamnan Jihar Legas a jamhuriya ta biyu. A wancan lokacin, akan ruwaito marigayi Shehu `Yar`aduwa yana mayar wa ’yan adawa da nasararsa, musamman na jihohin kudancin kasar nan da martanin cewa kar su zarge shi akan nasarar da ya samu, su zargi manyan `yan siyasar jihohinsu, don shi, su ya sa ni, kuma ta kansu ya bi ya kai ga nasarar. Ma`ana dai ta kungiyar kawancen siyasa ta PDM, ta kai labari.
Da aka dawo wannan jamhuriya, gyauron `yan kungiyar kawancen siyasa na PDM din dai su Allah Ya fara ba mulkin kasar nan, don kuwa sanin kowane cewa tsohon shugaban kasa babban aminin marigayi Shehu `Yar`aduwa ne, haka tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da Shugaba Obasanjon ya dauko ya rufa masa baya suka yi mulkin shekaru takwas, shi kansa kuma har gobe da wannan kungiyar adawa yake tutiya a siyasarsa. Shi ma tsohon shugaban kasa marigayi Alhaji Umaru Musa `Yar`aduwa kane ne ga Janar Shehu `Yar`aduwa albarkacin waccan tafiya ta `ya`yansa ya ci Cif Obasanjo ya dauko shi ya ba shi takara a PDP a zaben shekarar 2007, har ya zama shugaban kasa.  Mai karatu karewa ma da karau Alhaji Atiku Abukar har ya zuwa yau din nan shi ne Kwamanda Janar na kungiyar kawancen siyasa ta PDM, kuma ana zargin yana da hannu a cikin a nema wa PDM din rijistar rikidewa ta zama jam`iyyar siyasa, don kuwa shugaban wucin gadi na kasa baki daya na sabuwar jam`iyyar PDM din Alhaji Bashir Yusuf Ibrahim tshon mataimaki na musamman ne ga Cif Olusegun Obasanjo da shi  kansa Alhaji Atiku Abukar a lokacin da suke kan karagar mulki.
 Duk da Alhaji Atiku Abukar ya fadi cewa ba shi da hannu a cikin kafa wannan sabuwar jam`iyya ta PDM, har ya kara da cewa yana nan cikin tsohuwar jam`iyyarsa  ta PDP,  wai kuma ba zai iya hana na kusa da shi su yi ra`ayin dukkan siyasar da ransu ya kwanta masu, amma dai mutanen kasa da dama ba su yarda ba akan ba shi da hannu ko masaniyar kafa sabuwar jam`iyyar ta PDM. Shugaban tafiyar PDM  na kasa baki daya a zamanta na kungiyar kawancen siyasa Sanata Abubakar Mahdi da wasu daga cikin `yan kwamitinsa, an ruwaito su suna cewa su ba sa goyon bayan rikidewar PDM din  daga matsayinta wadanda suka kafata suka kuma tafiyar da ita. Amma kuma ka san a kome na rayuwa kowa da ra`ayinsa, don haka a cikin dai nasu akwai masu ra`yin  cewa haka din ya yi daidai, wai don koma yadda za su tunkari zaben 2015.
 PDM din ta zo a daidai lokacin da aka samu hadewar manyan jam`iiyyun adawa na kasar nan uku wato ANPP da ACN da CPC da wani bangare na jam`iyyar APGA, inda suka narke suka zama sabuwar jam`iyyar APC, don tunkarar babbar jam`iyyar ta PDP, a babban zabe na kasa a shekarar 2015, mai zuwa in Allah ya kaimu. Kafin bayyanar PDM din a zaman jam`iyyar siyasa, akasarin mutanen kasar nan masu akidar ganin an samu  canji daga mulkin PDP, da irin hayaniyar siyasar da ta kankama tsakanin wasu jiga-jigan jam`iyyar ta PDP ciki kuwa har ta gwamnonin nan biyar da suke kalubalantar neman sake tsayawa takarar shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan a zaben shekarar 2015, ana hasashen APC din za ta taka wata gagarumar rawa a zaden na gaba, duk da yake PDP ta ce ba ta hasashen wata barazana daga hadewar jam`iyyun adawar.
 Amma yanzu da bayyanar jam`iyyar PDM din, akwai matukar fargaba kan cewa za a ci gaba da  samun rarrabuwar kan `yan Arewa da kuri`unsu, da taimako da goyon bayan `yan Arewar masu kwadayin ana ha-maza-ha-mata sai sun mallaki kasar nan. Alal misali, kamar yadda na fadi tun farko, tuni wasu daga cikin `yan kungiyar kawancen siyasa ta PDM, suka ce ba za su bar PDP, don su koma PDM, amma kuma wannan ba yana nufin wasu ba za su bar PDP din da ita kanta sabuwar jam`iyyar APC ba zuwa PDM din. A takaice dai zuwan wannan  sabuwar jam`iyyar ta PDM ka iya cewa wata sabuwa ga `yan Arewa, don kuwa `yan Arewa ne kadai suke kada kuri`unsu a cikin zabubbukan kasar nan a tarwatse saboda son zuciyar shugabanninsu da rarrabuwa irin ta addini da kabilanci da sauransu.