✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata da ake zargin ta kamu da zazzabin Lassa ta mutu a asibitin Abuja

Wata mata mai suna Joy Nana Bashir, da ake jinyarta a asibitin garin Kubwa da ke Abuja, kan cutar da a ke zargin zazzabin Lassa…

Wata mata mai suna Joy Nana Bashir, da ake jinyarta a asibitin garin Kubwa da ke Abuja, kan cutar da a ke zargin zazzabin Lassa ce, ta mutu a yau Laraba.

Matar wadda aka garzaya da ita zuwa asibitin a ranar Lahadin da ta gabata wadda ’yar asalin garin Auchi ne da ke jihar Edo, an kaita asibitin ne daga kauyen Kagini da ke kusa da garin na Kubwa.

A lokacin da wakilinmu, ya isa asibitin ya ga yadda wani jami’in tsabta ke yin feshi a sashin hadurra da bukatar gaggawa inda a ka kwantar da matar tun a farko.

Babban Daraktan asibitin Dokta Muideen Lasisi, wanda ya tabbatar da mutuwar, ya ce an ajiye gawar Joy a dakin ajiye gawa na asibitin.

Shugaban asibitin wanda ya umarci iyalan matar da su hanzarta binne gawarta, ya ce an aika da samfuri da aka dauka daga jikinta zuwa babbar cibiyar magance yaduwar cututtuka ta shiyya da ke birnin Abuja, don yin gwaji.