✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata budurwa ce ’yar shekara 18, za ta shiga wanka, daga ita sai zani xaurin qirji a jikinta. Ta xauki bokiti ta nufi bayin wanka, kafin ta shiga bayi sai ta ji ana ta hayaniya a qofar gidansu. Sai ta ajiye bokitin, ta leqa waje sai ta ga ashe yayarta ce,

Zani ko jariri? Wata budurwa ce ’yar shekara 18, za ta shiga wanka, daga ita sai zani xaurin qirji a jikinta. Ta xauki bokiti ta…

Zani ko jariri?

Wata budurwa ce ’yar shekara 18, za ta shiga wanka, daga ita sai zani xaurin qirji a jikinta. Ta xauki bokiti ta nufi bayin wanka, kafin ta shiga bayi sai ta ji ana ta hayaniya a qofar gidansu. Sai ta ajiye bokitin, ta leqa waje sai ta ga ashe yayarta ce, wacce aka yi aurenta tun shekara xaya da rabi da suka wuce, ba ta zo ganin gidaba sai yau. Nan take murna ta kama budurwar, ta manca halin da take ciki na xaurin qirji, ta fita ta tarbi yayarta kuma ta karvi xanta jariri; ta fara wasa da shi. To, irin wasan da mata suke yi wa yara, sai ta wulla yaron sama, kafin ya dawo ta cafke shi sai aka samu matsala, zaninta ya kwance, ya faxi kasa kuma gashi babu komai a jikinta sai zanin. Nan fat a ruxe, ta fara tunanin cewa, shin ta zaninta za ta yi ta rufe jikinta ko ta yaron da ta jefa sama? 08064385252