✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasikar Sanusi ga Jonathan tsarin aiki ne ba siyasa ba

A wannan makon ne wata wasika da a ke zargin Mallam Sanusi Lamido Sanusi Gwamnan babban bankin Najeriya ya aikawa shugaban kasa Jonathan a watan…

A wannan makon ne wata wasika da a ke zargin Mallam Sanusi Lamido Sanusi Gwamnan babban bankin Najeriya ya aikawa shugaban kasa Jonathan a watan satumba ga me da bacewar wasu kudi ta fara zagayawa kafafen yada labarai, sai dai har zuwa yanzu babu tabbacin cewa gwamnan ne ya rubuta ko kuwa ‘yan siyasa ne domin kuwa an tabbatar ba rattababben sa hannun Malam Sanusi.
A cikin wasikar an ruwaito cewa; Alkaluman da babban bankin ya fitar na nuna cewa kudin man fetir din kasa tun daga shekarar
2012 har tsakiyar watan Yuli na 2013 sun bace. Alkaluman sun nuna cewa kashi 76 cikin 100 na kudin man Najeriya sun bace, wanda kashi 24 cikin 100 ne kawai na wadannan kudi suka shiga babban bankin Nijeriya wanda ake cewa kudin da ake cewa sun bace ya kai tiriyan takwas ta Naira, amma a kayyade dala biliyan 49.8 ne.
Wannan kudi da aka wawashe su ne mafi yawan kudi da aka taba wawashewa a Afirika.
Masu nazari na bayyana cewa wannan wasika dai ankararwa ce ga shugaban kasa bisa tsarin aiki ba wai bisa siyasa ba in har ma Malam Sanusin ne ya rubuta. Yayin da wasu ‘yan adawa kuma su ke ganin yunkuri ne na hambarar da gwamnatin, sanin kowa ne in har Malam Sanusi ne ya rubuta takaddar to, tabbas wannan shi ne ainahin gaskiya a na yiwa dukiyoyinmu handama da babakere.
A nan A rewacin Najeriya akwai mutane jarumai wadanda su ka kawo gyara da canji da ci gaba ga rayuwar al’umar wannan kasa. Mutane irin su Sir Ahmadu Bello, Abubakar Tafawa Balewa, Mallam Aminu Kano, da sauransu, wadanda suka taimaka aka kwato wa Kasar nan ‘yancin kai daga Ingila suka kuma tabbatar da cewa kasar Hausa ta zama jagora a kasar sun yi rawar gani matukar gaske. A wani barin kuma in ka kalli General Murtala Ramat Mohammed wanda duk da cewa bai jima akan karagar mulki ba, amma har yanzu ana cin gajiyar ayyukan da ya bijiro da su kafin Allah ya amshi ransa.
A yanzu Allah ya kawo mana Mallam Sanusi Lamido Sanusi dan Majen Kano ya dauko duk wadannan siffofin na wadannan iyayen namu da suka gabace shi ta wajen kishin kasa, jajircewa da nuna karfin hali wajen tabbatar da cewa an bi hanyar da ya kamata kuma an daina abubuwan da ba su kamata ba a duk harkokin kudi a wannnan kasa.
 Mallam Sanusi Lamido baya shakkar kowa kuma ba ya kyamar talakawa. Hasali ma in ka ganshi da wuya ka shaida cewa shi ne Gwamnan Babban Bankin kasa saboda babu wannan jan aji da shan iska da masu rike da madafan mulkin kasar nan ke yi. Sai dai nuna kamala da dattijantaka. Ga shi kuma ba ji da kai wai cewa dan sarauta ne ko kuma yana rike da wata babbar sarauta a masarautar Kano. Ko yaushe yana cikin raha da jan hira kamar dama can ya san mutum. Zai rika sa ka ji kamar kai ne a sama shi kuma yana kasan ka. Sai ka hadu da shi zaka san irin karimcinsa.
Mallam Sanusi Lamido Kwararre ne a sashinsa na aikin banki. Ya yi mun gani kuma mun shaida. Haka kuma mun tabbatar da cewa ba’a taba yin Gwamnan Babban Bankin Kasa na Najeriya kamar sa ba in aka duba irin aikin da yayi cikin dan karamin lokaci daga hawansa a shekarar 2009 zuwa yau.
Ya nuna kwarewa da bajinta in da yai maganin duk matsalolin da kasar nan ke fama da su ta fannin hada-hadar kudi da tattalin arziki. Aiki wanda wadanda suka gabata da shi suka gaza saboda jan aiki ne wanda in har dai za’a yi shi to kuwa za’a taka kafafuwan manya-manyan mutane a kasar wadanda suke ci da sha da shugabanninmu na can koli.
Ayyukan da Mallam Sanusi ya yi sai jarumi wanda ba ya tsoron kowa kuma baya tsoron komi. Sai mai gaskiya wanda ke kallon alkibla daya. Sai wanda abun duniya bai tsone masa ido ba. Babban aikin da Mallam Sanusi ya yi shine na gyara da tsaftace bankunan kasar nan. Wannan babbar nasara ce saboda albarkacin hakan ne ya tabbatar da samun wadansu nasarorin a wannan kasar tamu.
bangaren bankuna a kowace kasa yana kan muhimmiyar matsaya saboda a duk lokacin da aka samu matsala a wannan bangare arzikin kasa yana girgiza. Shi yasa duk duniya ake kafa-kaffa da wannan sashe.
Dan a tabbatar da nagartar wannnan sashe da kuma cewa yana cikin koshin lafiya a ko yaushe ya zama dole a ci gaba da futo da sababbin hanyoyi, na baya kuma a ci gaba da yi musu garanbawul.
Aminiu Sadauki ya rubuto daga Gida mai lamba 42b, Kofar Mata Kano.