✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasan sada zumunta: Super Eagles ta lallasa Ludembourg

A ranar Talatar da ta wuce ne kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta lallasa kasar Ludembourg da ci 3-1 a wasan sada zumunta.  Haka…

A ranar Talatar da ta wuce ne kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta lallasa kasar Ludembourg da ci 3-1 a wasan sada zumunta.  Haka kuma a ranar Juma’ar da ta gabata ma kungiyar ta samu nasara a kan Mali da ci 1-0 a wani wasan sada zumuntar.
Yanzu dai kungiyar ta samu nasara a wasannin sada zumunta biyu kenan da ta yi da kasashen a tsakanin mako guda.
’Yan kwallon Super Eagles Brown Ideye da Kelechi Iheanacho da kuma Odion Ighalo ne suka samu nasarar zura kwallayen a ragar Ludembourg a wasan.
Tuni magoya bayan kungiyar Super Eagles suka shiga tofa albarkacin bakinsu a kan nasarar da kungiyar ta samu a karkashin jagorancin Salisu Yusuf. Yayin da wadansu suke goya wa kocin rikon kwarya na kungiyar Salisu Yusuf baya, wasu kuwa nuna shakkunsu suka yi akan kwarewar kocin duk da ya samu nasara a wasannin biyu da ya yi.
Har yanzu dai ana dambarwar  yiwuwar daukowa kungiyar Super Eagles sabon koci daga waje, inda wasu suka goyi baya, yayin da wasu kuma suke nuna shakku.