Mutanen yankin Ikotun da ke Jihar Legas sun ga tashin hankali a ranar da aka yi wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da takwararta ta Atletico Madrid yayin da wani matashi mai suna Yemi ya kashe Saheed Badmus lokacin da suke fada a gidan kallon kwallo da ke layin Lamina a yankin Ikotun.
Hakazalika wani matashi mai suna Destinya Ameh ya rasa ransa yayin da wani wanda ba a gano shi ba ya sare shi da adda a lokacin da yake murnar cin kwallo a wasan Chelsea da Atletico Madrid a gidan kallon kwallo na unguwar Badagiri da ke Jihar Legas.
Lamuran biyu sun auku ne a ranar da aka yi wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da takwararta ta Atletico Madrid a makon da ya gabata.
Aminiya ta gano cewa Yemi ya cakawa Saheed Badmyus kwalba ne yayin da suke kokawa inda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.
Wani wanda lamarin ya auku a kan idonsa mai suna Waheed ya bayyana cewa ‘Suna cikin musu sai kawai aka turo su waje aka kulle kofar gidan kallon sai suka ci gaba da dambe sai Yemi ya dauko kwalba daga wani shago ya fasa ya cakawa Saheed a ciki. Nan take muka dauke shi kafin mu kai shi asibiti ya mutu’.
Ya ci gaba da cewa ‘Yemi yana ganin ya yi masa illa sai ya gudu, muka sanar da ’yan sanda su kuwa suka kama shi a gidan maihaifinsa inda ya buya. Yanzu haka yana can wurinsu suna yi masa bincike. Da ma Yemi ya saba yi wa mutane rauni’.
Aminiya ta gano cewa Amey ya mutu nan take a lokacin da wani ya buga masa adda mai kaifi a tsakiyar kansa a lokacin da yake murnar cin kwallon da aka yi a wasan.
Wani wanda lamarin ya auku a kan idonsa wanda bai so a bayyana sunansa ba ya bayyana cewa ‘Muna tsakiyar kallo sai aka ci kwallo sai kawai Ameh ya tashi yana ihu sai wani matashi ya buga masa adda mai kaifi a tsakiyar kai sai wuri ya rude aka rika rige-rigen fita daga gidan kallon ta haka wanda ya yi saran ya gudu. Nan take Ameh ya fadi cikin jini kafin a kai shi asibiti ya mutu’.
Sai dai wata majiya ta tabbatar da cewa an kai shi asibitin bictoriya da ke yankin Badagiri inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
’Yan sanda sun tabbatar da aukuwar lamuran guda biyu kuma sun tabbatar da cewa suna gudanar da bincike.
Wasan Chelsea da Atletico ya janyo mutuwar mutum biyu a Legas
Mutanen yankin Ikotun da ke Jihar Legas sun ga tashin hankali a ranar da aka yi wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da takwararta ta…