✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasan Aljeriya da Najeriya: FIFA ta ci ta zaftare wa Super Eagles maki

Hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) a shekaranjiya Laraba ta bayar da sanarwar cin tarar Najeriya kimanin Naira Miliyan 2.  Baya ga tarar hukumar ta…

Hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) a shekaranjiya Laraba ta bayar da sanarwar cin tarar Najeriya kimanin Naira Miliyan 2.  Baya ga tarar hukumar ta umarci a zaftare maki 1 daga cikin maki 14 da kungiyar Super Eagles ta hada a yayin gudanar da wasannin neman hayewa gasar cin kofin duniya a Rasha.

Kenan yanzu Najeriya ta hada maki 13 ne maimakon 14 da ta hada tun da farko kafin a yanke wannan hukunci.

FIFA ta ce ta dauki wannan mataki ne ganin yadda kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta sanya dan kwallonta Shehu Abdullahi a wasan duk da kasancewa yana da katin gargadi biyu (yellow card) a jere da hakan ta sa bai cancanci ya buga wasan ba.

Bayan an kammala wasan ne sai kasar Aljeriya ta kai karar Najeriya a game da sanya dan kwallon da bai cancanci buga wasan ba.  Bayan FIFA ta yi bincike ne sai ta gano Najeriya ta yi laifi inda ta dauki matakin rage mata maki daya da kuma cin tarar kasar Naira Miliyan 2 don ya zama darasi.

Sai dai duk da wannan hukunci Najeriya ce za ta halarci gasar cin kofin duniya a Rasha daga rukunin B inda yanzu ta hada maki 13 sai Zambiya da ke biye da  maki 8 sai Kamaru mai maki 7 yayin da Aljeriya kuma ta hada maki 4 maimakon maki biyun da ta hada tun da farko.

Kenan bayan FIFA ta zaftare maki 1 ga makin Super Eagles ita kuwa Aljeriya an kara mata maki biyu ne, watau yanzu ta hada maki 4 kenan maimakon maki 2.

Tuni Shugaban Hukumar NFF Amaju Pinnick ya ce za su gudanar da bincike  don zakulo wadanda suke da hannu game da wannan badakala wato na amfani da Shehu Abdullahi a wasan Najeriya da Aljeriya duk da kasancewa bai cancanci buga wasan ba.