✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wankan rafi ya yi ajalin ‘yar shekara 15 a Kano

Wata budurwa mai shekara 15, Humaira Muhammad, ta mutu yayin wankan rafi a kauyen Dandanko da ke Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano. Mai magana…

Wata budurwa mai shekara 15, Humaira Muhammad, ta mutu yayin wankan rafi a kauyen Dandanko da ke Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano.

Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana a Jihar, Alhaji Saminu Abdullahi ne ya tabbatar hakan yayin ganawarsa da manema labarai a ranar Laraba.

“Da misalin karfe 12:39 na ranar Laraba muka samu kiran gaggawa daga wani Nasa’i Abba.”

“Bayan samun kiran ne muka yi azamar tura tawagar kai dauki ta ma’aikatanmu zuwa wurin domin tsamo gawar budurwar.”

“Mun ajiye gawar a gidan Dagacin kauyen ‘Yan Sama da ke Karamar Hukumar Kumbotso, Alhaji Mukhtar Abdullahi,” a cewar sanarwar.

Saminu ya ce ajali ne ya yi kiran Marigayiya Humaira wacce ta je wankan rafi kuma ta nutse a cikinsa.

Kazalika, ya yi kira ga al’umma da su rika tsawatar da ‘ya’yansu a kan zuwa wankan rafi da sauran wurare masu hatsari.