✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano

Hukumar ta ce tuni aka miƙa gawar mamacin ga dagacin ƙauyen.

Wani mutum mai shekaru 50, mai suna Yusuf Nadabo, ya rasu bayan da rijiya ta rufta masa yayin da yake gyaranta a ƙauyen Gargajiga da ke Ƙaramar Hukumar Minjibir a Jihar Kano.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce an ceto Yusuf daga rijiyar ba ya cikin hayyacinsa, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.

A cewar Abdullahi, “Mun samu kiran gaggawa daga Bashir Namadi, wanda ya sanar da ruftawar rijiya a kauyen Gargajiga.

“Mutum uku lamarin ya shafa yayin da ake gyaran rijiyar. Ɗaya na cikin rijiyar, sai kuma mutum biyu da ke waje.

“Wasu sashen rijiyar sun rufta, wanda hakan ya rufts da mutanen da ke wajen rijiyar tare da rufe wanda ke ciki.”

Hukumar ta isa wajen cikin gaggawa kuma ta samu nasarar ceton mutum biyu da ransu.

Amma Yusuf Nadabo, wanda ya maƙale cikin rijiyar, an same shi ba ya cikin hayyacinsa, kuma daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa.

Abdullahi ya ƙara da cewa dukkanin waɗanda abin ya shafa an miƙa su ga dagacin ƙauyen Gargajiga.