✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani barawo 1

Wani barawo ne ya shiga wani gida sata, gidan daki da falo ne. Gidan an dauke wuta, yana shiga falon sai ya tarar da maigidan…

Wani barawo ne ya shiga wani gida sata, gidan daki da falo ne. Gidan an dauke wuta, yana shiga falon sai ya tarar da maigidan yana barci, ya ajiye wata sabuwar adda a gabansa. Sai barawon nan ya lallaba ya dauke wannan addar, ya samu wani waje a cikin gidan ya rataye ta, don gudun kada idan mai gidan ya farka ya dauke ta ya far masa. To ashe duk abin da yake, maigidan ba barci yake ba, yana kallonsa saboda dakin duhu ne da shi. Kai tsaye sai barawon nan ya wuce daki don yin abin da ya kawo shi. Bayan ya gama satar nan, yana zuwa falon nan sai ya yi niyyar ya dauke wannan addar ya tafi da ita, yana zuwa wajen inda ya ajiye ta sai ya tarar an zare addar daga gidanta, sai gidan kawai a rataye. Sai ya dauko cocilan dinsa ya dan haska inda maigidan yake sai ya ga ba ya nan. Daga nan ne barawon ya fara fitar da kayan da ya sato yana ajiyewa, yana cewa: “Wallahi ban dauki komai ba, don Allah ka yi hakuri, wallahi ga kayan nan.” Da ma dakin duhu ne da shi, nan take sai ya ji caraf, an kama shi.

Daga Isah Ramin Hudu Hadeja 08060353382