✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani barawo

Wani barawo ne ya je wani gida sata, yana zuwa sai ya kwankwasa kofar gidan. Nan take maigidan ya amsa, ya ce: “Wane ne?” Ya…

Wani barawo ne ya je wani gida sata, yana zuwa sai ya kwankwasa kofar gidan. Nan take maigidan ya amsa, ya ce: “Wane ne?” Ya ce: “barawo ne kuma na zo na yi sata.” To, dama a gaban gidan akwai wata taga sai maigidan ya dauko wata adda ya jefo ta wannan tagar, ya ce wa barawon: “dauki wannan addar kafin na zagayo!” Da barawon nan ya ga har mai gidan nan ya ba shi adda sai ya yi zaton lallai yana da kyakykyawan shirin da ya fi nasa. Nan take ya ruga da gudu.
Daga Isah Ramin Hudu, Hadeja 08060353382.