✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wane ne magajin Gwamna Kwankwaso a jam’iyyar APC?

Jihar Kano na cikin jihohi da gwamnanta Injiniya Dokta Muhammadu Rabi`u Musa Kwankwaso, shugaban darikar siyasarsa ta Kwankwasiyya (a cikin kowace jam`iyya da ya samu…

Jihar Kano na cikin jihohi da gwamnanta Injiniya Dokta Muhammadu Rabi`u Musa Kwankwaso, shugaban darikar siyasarsa ta Kwankwasiyya (a cikin kowace jam`iyya da ya samu kansa), zai bar karagar mulki a shekarar mai zuwa, saboda kasancewar wannan shi ne karonsa na biyu da yake Gwamnan Kano kamar yadda Kundin tsarin mulkin kasar nan na shekarar 1999, da akai yi wa kwaskwarima ya tanada, bayan ya yi zangonsa na farko tsakanin 1999 zuwa 2003, da yake fuskantar kalubalen wa zai gaje shi

Kafin in yi nisa a cikin wannan makala, ya kamata in dan yi wa mai karatu matashiya akan wane ne Gwamna Rabi`u Kwankwaso a fagen siyasar Jihar Kano da ma ta kasa da a yau ake ta ambatonsa a cikin jerin sunayen masu neman yi wa jam`iyyarsu ta APC takarar neman shugabancin kasar nan a zaben badii in Allah Ya kaimu. Tararuwarsa a fagen siyasa ta fara haskawa a shekarar 1991, lokacin da ya ci zaben dan Majalisar Tarayya na mazabar tarayya ta Kura da Garun Malam da Madobi a jamhuriya ta uku ta Janar Babangida da ba ta kai labari ba, har kuma ya zama mataimakin Kakakin Majaisar a wancan lokacin.
Da aka dawo da harkokin siyasa gada-gadan a shekarar 1998, Gwamna Kwankwaso na cikin mutanen da suka kafa jam`iyyar PDP, har kuma Allah Ya ba shi nasara ya samu tsaya mata takarar neman mukamin gwamnan jihar, ya kuma yi nasarar a zabubbukan 1999, ya kuma yi mata gwamnan shekaru hudu kamar yadda na ambata a sama. Bayan bai yi nasarar sake dawowa akan kujerarsa ba, a shekarar 2003, lokacin da tsohon babban Sakatare a gwamnatinsa Malam Ibrahin Shekarau da ya yi wa jam`iyyar hamayya ta APP, a lokacin takara ya kayar da shi. Gwamnatin tsohon shugaban kasa Cif Obasanjo ta PDP, bayan ta sake cin zabe a karo na biyu ta yi wa tsohon gwamnan Ministan Tsaro, bayan ya sauka daga kan mukamin Minisata ya rike mukaman mai bai wa shugaban kasa shawara a yankin Dafur na kasar Sudan. Daga bisani ya yi Darakta a Hukumar raya yankuna masu arzikin man fetur a yankin Neja-Delta.
Ya yi kokarin ya dawo ya nemi mukamin Gwamnan Jihar Kano a shekarar 2007, a inuwar tsohuwar jam`iyyarsa ta PDP, amma wasu dalilai da suka bijiro masa a lokacin suka sa ala tilas ya janye ya nuna Alhaji Ahmed Garba Bichi, wanda shi ya tsaya takarar da Gwamna Malam Ibrahim Shekarau, wanda Allah bai sa Alhaji Ahmed din ya yi nasara ba.
Gwamna Kwankwaso ya ci gaba da yin hobbasa wajen ganin ta kowane hali ba`a raba shi da shugabanci jam`iyyarsu ta PDP ba, don haka irin yadda ya iya rike jam`iyyar gam tun yana gwamna a shekarar 1999 zuwa 2003, da rana daya bai taba yin sanya ba, har ya dawo kujerarsa ta gwamnan a shekarar 2011, duk kuwa da a cikin PDP din akwai jiga-jiganta irinsu tsohon Minista Alhaji Musa Gwadabe da marigayi tsohon Gwamna Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi da Minista Ambasada Aminu Wali da dai suransu.
A kusan karshen shekarar da ta gabata ne Gwamna Kwankwaso ya kasance cikin gwamnoni biyar na jam`iyyar PDP da suka canja sheka zuwa sabuwar jam`iyyar gamayyar jam`iyyun adawa na ANC da APGA da ANPP da CPC da suka narke suka kafa jam`iyyar APC, jam`iyyar da a jiya Alhamis Gwamna Kwankwaso ya bayyana aniyarsa ta shiga cikin jerin `yan takarar da suke son ta sahale musu ta tsayar da shi takarar neman shugabancin kasar nan a zabubbukan shekara mai zuwa.
Mai karatu wannan shi ne dan takaitaccen tarihin Gwamna Kwankwaso a fagen siyasar kasar nan, gwamnan da yake alfahari da yi wa birni Kano da sauran yankunanta, ayyukan raya kasar da aka dade ba a yi masu ba, musamman gadojin sama da ba wani babban birnin jiha a arewacin kasar nan da ma na wasu jihohin kudancin da ya taba samun tagomashinsu, baya ga bayar da tallafi ga masu sana`o`i da tura yara karo ilmi a ciki da wajen kasar nan da dai sauran ayyuka. Kodayake ayyukan gina hanyoyi masu tsawon kilomita biyar-biyar da aka fara a dukkan Hedkwatocin kananan Hukumomin jihar 44, yau sama da shekaru biyu akasarinsu suna neman gagarar Gwamnatin Kwankwason.
Da wancan dan tarihi na siyasar Gwamna Kwankwaso da yadda ya dawo mulkin Kano a karo na biyu da ayyukan da ya gudanar da canjin shekar da ya yi daga PDP zuwa sabuwar jam`iyyar APC, da yadda ya gudanar da zabubbukan kananan Hukumomi a watan Afrilun da ya gabata (zabubbukan da duk da sauran `yan jam`iyyun hadakar APC sun nuna kwadayin su tsaya takarar neman shugabancin kananan Hukumominsu, da kyar wasu suka samu mukaman mataimaka), wadannan duk za su tabbatar wa mai karatu cewa sai wanda Gwamna Kwankwaso ya ga dama ya mara wa baya zai samu wannan takara a inuwar jam`iyyarsu ta APC.
Yanzu maganar da ake yi daga bangaren darikar Kwankwasiyya ta Kwankwaso, mataikinsa (wanda suke tare a harkokin siyasa tun shekarar 1999), shi kadai ya fito karara yake yakin neman zaben ya gaji Gwamna Kwankwaso. Sauran `yan Kwankwasiyya irin su Sakataren gwamnatin jihar Injiniya Rabi`u Sulaiman Bichi da Kwamishinan Ayyuka Alhaji Abba Kabir Yusuf da tsohon Ministan Ciniki Alhaji Ahmed Garba Bichi, duk sun yi shiru, suna kuma jiiran su ji daga bakin gwamna Kwankwaso akan wa zai nuna .
Daga `yan asalin hadakar kafuwar jam`iyyar APC, akwai `yan takara irin su Janar Lawan Ja`afar Isah, tsohon Gwamnan Mulkin Sojan Jihar Kaduna da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da mataimakin Bulaliyar Majalisar Wakilai Alhaji Abdurrahaman Kawu Sumaila da Alhaji Usman Alhaji, wadannan, tuni jirgin yakin neman zaben akan neman takarar mukamin Gwamnan jihar ya yi nisa cikin tafiyar neman biyan bukatarsu, bisa ga karan kansu, ba tare da suna amfani da batun darikar Kwankwasiyya ba. Baya ga sauran `yan taka-kara da nemansu bai wuce ta kafofin yada labarai ba.
Masu iya magana kance “dabara ta rage wa mai shiga rijiya”, tabbas ba wai a Jihar Kano kadai ba, a kowace jiha kuma a kowace jam`iyya gwamnonin jihohi na da muhimmiyar rawar takawa wajen yin nune da tabbatar da nasarar wanda zai gaje su, koda kuwa bayan sun yi nunen dan takarar ta su ba zai kai labari ba, kamar yadda aka gani a baya. Haka batun yake da bayan an yi nunen sai ka ga cikin wani kankanen lokaci an ja dagar da za ta kai ba a ga maciji tsakanin tsohon gwmna da yaronsa.
Da wannan nike ganin ya kamata Gwamnan Kwankwaso kamar yadda ya yi ta alkawarin zai bari jam`a su darje dan takarar da ya kwanta musu, amma ba ya dage akan sai ya yi nune ba. Masu iya magana kan ce gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah, Kwankwaso dai ya ga irin yadda aka karke tsakanin tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Sanata Ahmad Sani da tsohon mataimakinsa kuma wanda ya gaje sa Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafa, ya kuma ga yadda karewa da karau ake karke tsakanin da da uba, wato marigayi Sanata Olusola Abubakar Saraki da dansa Sanata Bukola Abukar Saraki. Nune ko kusa baya ci, bare a wannan karon a Jihar Kano a cikin `yan darikar Kwankwasiyyar kanta, akwai da yawa da suka sha alwashin muddin Gwamna Kwankwaso bai masu adalci ba, to, su kuma a shirye suke su yakesa, ta yadda kowa zai rasa. Me ke abin kankanewa? Shi kanshi mulkin dimokuradiyya takensa shi ne “Mulkin jama`a daga jama`a domin jama`a.” Allah ka bamu ikon zaben shugabanni na gari da za su yi mana mulkin adalci tun daga sama har kasa.