✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wandon mawaki Asake ya barke yana tsaka da rawa a kan dandamali

Wandon fitaccen mawakin Najeriya, Ahmad Ololade, wanda aka fi sani da Asake, ya yage yana tsaka da waka kan dandali a London. Lamarin ya auku…

Wandon fitaccen mawakin Najeriya, Ahmad Ololade, wanda aka fi sani da Asake, ya yage yana tsaka da waka kan dandali a London.

Lamarin ya auku ne yayin da mawakin yake rera wakar ‘Loaded’ da suka yi tare da fitacciyar mawakiyar Najeriya Tiwa Savage, inda ya cilla kafarsa a wani salon rawa, kuma hakan ya sa wandonsa take ya yage har farin dan kamfansa ya bayyana.

Daga nan ne cikin jin kunya ya ci gaba da rawa yana ja baya, har ya bar dandalin.

Tuni dai bidiyon ya gama karade kafafen sada zumunta, inda wasu suka fara sanya bidiyon kwaikwayonsa, ta hanyar yaga wandunansu, da sanya farin dan kamfai a ciki.