✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wanda ya yi wakar ‘Najeriya Jaga-jaga’ ya kamu da ciwon koda

Za a yi masa aikin ne a karshen watan Yuli

Za a yi wa fitaccen mawakin nan da ya yi wakar nan da ta taba yin tashe a shekarun baya ta ‘Najeriya Jaga-jaga’, Eedris Abdulkareem, aikin dashen koda saboda lalurar da daya daga cikin kodojin nasa take fama da ita.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kamfaninsa na Lakeem Entertainment Inc ya fitar.

Sai dai sanarwar ta ce tsawon lokaci, an rika yi wa mawakin wankin koda a wani asibiti da ke Jihar Legas.

“Mamallakin kamfanin Lakeem Entertainment Inc. ya kamu da ciwon koda kuma ya jima ana yi masa wankin kodar a wani asibiti a nan Jihar Legas, Najeriya,” inji sanarwar.

Ana sa ran za a yi masa aikin ne a karshen watan Yuli.

Sun ce, “Yanzu an sa ranar yin tiyatar a karshen wannan watan na Yuli, kuma tuni aka kammala shirye-shirye da gwaje-gwaje, ciki har da na tabbatar da cewa kodar (wacce wani dan uwansa ya ba shi gudunmawa) ta dace.”

Daga nan sai kamfanin ya roki sauran ’yan Najeriya da su taimaka masa da addu’ar ganin an yi dashen cikin nasara.