✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wanda ya sace jikan Sheik Dahiru Bauchi ya shiga hannu

An kama mutumin da ya yi garkuwa da jikan shahararren malamin addinin Musulunci a Najeriya Sheik Dahiru Bauchi. Jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS)…

An kama mutumin da ya yi garkuwa da jikan shahararren malamin addinin Musulunci a Najeriya Sheik Dahiru Bauchi.

Jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) sun kubutar da yaron mai shekara uku sannan suka kwato kudin fansar da aka biya.

Darektan DSS na jihar Kano Muhammad Alhassa ya ce an kama mai garkuwan ne a wani otal bayan kwana biyar da aika-aikan.

An sace yaron mai shekara uku ne a ranar Asabar da Sheikh Dahiru Bauchi ya jarogranci sallar idi a garin Bauchi.

Darektan DSS din ya ce wanda ake zargin ya nemi a ba shi kudin fansa naira miliyan 10.

Daga baya ya rage zuwa miliyan shida kuma an tura masa miliyan 2.5 ta banki.

“Mun kai samame a otal din ke Sabon Gari inda muka kama Umar yana ajiye da yaron da ya sace.

“Yaron na cikin koshin lafiya kuma mun kwace kudin fansar da Umar Ahmad ya ciro daga banki,” inji  Muhammad.

Ya ce sun kai samamen ne bayan Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Habu Sani ya kai musu bayanan sirri.

Muhamamd ya kara da cewa wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.