Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya sake zama zababben dan Majalisar Dattawa mai wakiltar shiyyar Sakkwato ta Arewa a karo na uku.
Wamakko na jam’iyyar APC ya samu nasarar ce inda ya doke abokin karawarsa kuma Mataimakin Gwamnan Sakkwato, Mannir Muhammad Dan Iya na jam’iyyar PDP.
Kamar yadda Baturen Zaben, Ibrahim Magawata ya sanar, Wamakko ya samu nasara ne da rinjayen kuri’u 141,468 yayin da Dan Iya ya samu kuri’u 118,445 a karashen zaben kujerar Sanatan Sakkwato ta Arewa da Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta kammala a ranar Asabar.
Ana iya tuna cewa, bayan INEC ta gudanar da zaben tun a ranar 25 ga watan Fabrairu, ta ayyana cewa zaben bai kammala ba sakamakon wasu dalilai da suka hada rikici da aringizon kuri’u.
Wamakko wanda shi ne jagoran jam’iyyar APC a Sakkwato, ya yi gwamnan jihar har karo biyu kuma daga bisani ya tafi Majalisar Dattawa inda a yanzu ya samu nasarar wa’adi na uku.