✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Walla ba ka da diya

Wani Buzu ne ya shigo gari, sai ya ga wani magidanci a kofar gidansa, ’ya’yansa kanana sun baibaye shi suna ta nishadi, sai abin ya…

Wani Buzu ne ya shigo gari, sai ya ga wani magidanci a kofar gidansa, ’ya’yansa kanana sun baibaye shi suna ta nishadi, sai abin ya burge shi, ya matsa kusa da mutumin ya ce masa: “Walla, maigida, wadanga duk diyanka na?” Ya ce masa duk ’ya’yansa ne. Ya ce masa: “Duk diyanga sun yi ciwon kyanda?” Ya ce masa ba su yi ba. Sai Buzu ya ce: “Walla in dai diyanka ba su yi kyanda ba, to ba ka da diya, domin ni diya goma gare ni, amma duk kyanda ta gama da su.”
Daga A. A. Azare, Agege, Legas, 08066888222