✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wakokin Hip-Hop za su danne wakokin Hausa – G-BOY

Aminu Abdullahi  wanda aka fi sani da Prince G-Boy matashin mawakin Hip-Hop ne a Jihar Kano, a tattunawarsa da Aminiya ya bayyana cewa yana hangen…

Aminu Abdullahi  wanda aka fi sani da Prince G-Boy matashin mawakin Hip-Hop ne a Jihar Kano, a tattunawarsa da Aminiya ya bayyana cewa yana hangen nan ba da dadewa ba wakokn Hip-Hop za su danne dukkanin wakokin Hausa, sakamakon karbuwa da suka kara yi wajen jama’a.  Haka kuma mawakin yay i kira ga mawakan da su rika tsaftacewa tare da zabar kalaman da za su. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

 

Aminiya: Za mu so jin tarihin rayuwarka?

G-Boy: Sunana Aliyu Abdullahi Abdulhamid wanda aka fi sani da G-Boy a hakar wakokin Hip-Hop. An haife ni a unguwar Yalwa cikin Jihar Kano. Na yi karatun Firamarena a Makarantar Firamaren Yalwa  a wannan makarantar na yi karamar sakandire. Bayan na gama sai na tafi babbar sakadire a Makarantar Sakandiren Gwamnati ta Dala inda na kammala a shekarar 2014. A yanzu haka ina kokarin gyara jarrabawata yadda zan sami damar ci gaba da karatuna duba da cewa sai da ilimi mutum za iya yin komai na rayuwa, koi ko ita harkar wakar ta fi tafiya idan mutum yana da ilimi. 

Aminiya: Ya aka yi ka fara waka?

G-Boy: Zan iya cewa tun farko ni mai son wakoki ne don ina yawan saurarensu. Daga nan ne kuma ra’ayin yin wakar ya shige ni har ma na tsinci kaina da fara rubuta tare da rera wakoki. Zan iya cewa na fara rubuta waka a shekarar da na kammala makaranta wato a 2014. Da farko ina rubuta wakokin ne na rika rerawa a haka. Amma a yanzu a kwana a tashi na sami wadanda suke yi min recording wato double S inda nake gudanar da ayyukana a karkashinsu. 

Aminiya: Wakoki nawa ka yi kuma mene ne jigon wakokinka?

G-Boy: Ina yin wakokin raf, sai dai a yanzu na fi yin R&B. Haka kuma idan ta kama ina yin wakokin nanaye. Abin da muke dubawa shi ne bukatar al’umma. Babu shakka na rubuta wakoki da dama wadanda ke ajiye da ba abuga ba za su kai 18. Sai dai a yanzu an buga wasu kamar su My mother da Lokacina da  Me & You da Zo mu je da Let them know da sauransu. Amma idan zan lissafa har da  wakokin da na yi tare da wasu jama’a wakokina za su kai 35. Duk da cewar ban riga an yi albam nawa na kaina ba, amma wakokina suna cikin albam din tarayya na abokan aikina. Amma in Allah Ya yarda a sabuwar shekara nan mai kamawa zan yi albam nawa na kaina. Zan iya cewa fadakarwa shi ne jigon wakokina, domin yawanicn wakokina ina yin su ne a kan wani abu da ke damun al’mma. Ita waka hanya ce mai sauki wajen isar da sako sakamakon sauraren waka da mutane key i, to idan mutum ana da wani abu da yake so ya fadakar da jama’a kai sai mu yi amfan da hanyar waka.misali abubuwa irinsu fyade da barace-barace da rashin ilimi da sauransu. A yanzu haka an saki wata sabukar wakata mai taken ‘BA MARAYA’ wacce ke nuni akan muhimamncin dogaro da kai.

Aminiya: Wane kira kake da shi ga ’yan uwanka mawaka?

G-Boy: Ina kira ga ’yan uwana mawaka da mu daina amfani da damar waka muna bata tarbiyyar jama’a tare da yin zantuttuka wand aba su dace ba. mu sani cewa idan muka tsaftace harshenmu wajen fitar da kalamai  masu kyau shi zai sanya al’umma su kara karbar wakokinmu.  Haka kuma idan aka tsaftace kalmia, zai iya yiyuwa har a manyan makarantu za a rika yin nazarin irin wadannan wakokin. Ina ganin anan gaba wakokin Hip-Hop za su iya danne duk wasu wakoki na Hausa a fadin kasar nan.

Aminiya: Wane kira kake da shi ga gwamnati?

G-Boy: Ina kira ga gwamnati da ta taimaka mana duk da dai ana cewa idan ambu yay i yaw aba ya jin mai, amma dai yawanmu ba zai hana gwmanati ta taimaka mana ba. Sanin cewa a yanzu abubuwa ba su tafiya sai da kudi. Za ki tarar cewa idan mutum yana da basira yana kuma da kudi sai kika abubuwna suna tafiya daidai, sabanin wanda ke da basira ba shi da kudi. Muna bukatar gwamnai ta duba cewa mu muna samarwa da kanmu aikin yi ne ta hanyar yin waka, don haka muna bukatar ta tallafa mana. Haka kuma akwai bukatar ta rika ba mu kwarin gwiwa ta hanyar shirya mana tarurruka na bayar da lambar yabo wanda zai sa mu san gwamnati ta san da mu.