Hudubar Imam Abdulmumin Ahmad Khalid
Masallacin Badar, Kubwa Phase II, Abuja
Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman taimakonSa muna neman gafararSa da shiriyarSa. Wanda Allah Ya shiryar shi ne shiryayye, wanda Ya batar babu mai shiryar da shi. Muna neman tsarinSa daga miyagun ayyukanmu da sharrukan kawunanmu.
Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da cancanta sai Allah! Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya. Ina shaidawa cewa Annabi Muhammad bawanSa ne, kuma ManzonSa ne. Tsira da aminci su tabbata a gare shi, da ’yan dakinsa da alayensa baki daya.
Bayan haka ya bayin Allah masu girma! Ku ji tsoron Allah matukar jin tsoronSa. Kada ku mutu sai kuna Musulmi. Ku kyautata dangantakarku, ku sadar da zumunta domin wajiba ce a Musulunci.
Allah (SWT) Ya ce: “Ku bautawa Allah, kada ku hada Shi da kowa. Iyaye kuma ku kyautata musu da ’yan uwanku na kusa……….” (Suratun Nisa’i: 36).
Allah (SWT) Ya ce: “Wadanda suke sadar da abin da Allah Ya ce a sadar (zumunta)………” (Suratur Ra’ad: 21).
Anas Bn Malik (RA) ya ruwaito Hadisi Annabi (SAW) yana cewa: “Duk wanda yake so Allah Ya yalwata masa arzikinsa, ya bar baya (tarihi) mai kyau! To ya sadar da zumuncinsa.” Bukhari/Muslim.
A’isha (RA) ta ruwaito Annabi (SAW) yana cewa: “Zumunci na makale da Al-arshin Ubangiji, yana cewa: (Ya allah) wanda ya sadar da ni, Ka sadar da shi (rahamarka). Wanda ya yanke ni Ka yanke shi (da rahamarka).” Bukhari/Muslim
Abu Huraira (RA) ya ruwaito cewa: “Wani mutum ya zo wurin Annabi (SAW) yana tambaya game da zumunci. Ya ce: “Ina da ’yan uwa, ni ina sadar da zumuncina a gare su, amma su suna yanke ni, ina kyautata musu, su kuma suna munana mini, suna yi mini wauta ni ina hakuri da su. Sai Annabi (SAW) ya ce: Idan dai abin da ka fada haka ne, to kamar kana ciyar da su toka mai zafi ne (zunubi). Idan ka (daure) ka ci gaba, Allah zai daukaka ka a kansu.” Muslim.
Wato mutum zai ci gaba da zumunci da ’yan uwansa, koda su ba su yi, shi yana samun lada da daukaka, su kuma suna daukar zunubi na kin yin abin da Allah Ya yi umurni da shi. Kuma shi sadar da zumunci, ko addini ya bambanta ana yin sa. Musulunci bai hana ba, ba babba ba karami, ba mai wadata, ba talaka, ba na birni ba na kauye. Kowa zai iya ziyartar kowa, ya yi masa zumunci. Lokacin da Abu Dalha (RA) ya fahimci ma’anar ayar “Lan tanalul birra……..” (Ali-Imran: 92).
Cewa ba za ku samu tsoron Allah ba har sai kuna ciyarwa daga dukiyarku da kuke so. Yana da gona hudu sai ya bayar da daya sadaka sai Annabi (SAW) ya ce masa je ka raba wa ’yan uwanka na kusa. Sai ya raba ta ga ’yan uwansa da ’ya’yan baffanninsa.
Wadansu mata sun zo wurin Annabi (SAW) suna tambaya game da sadaka, cewa suna da kayan ado, suna so za su yi sadaka da su. Suna iya bai wa mazansu da marayun da ke karkashin kulawarsu? Sai ya ce, yin hakan za su samu lada biyu ne. Ladar zumunci da ladar sadaka.” Bukhari/Muslim
Maimunatu Bintul Haris (RA) ta ’yanta baiwarta sa’annan ta sanar da Annabi (SAW). Sai ya ce mata: “Da kin ba da ita ga ’yar uwar mahaifiyarki da ya fi lada.” Bukhari/Muslim.
Ya ’yan uwa! Ku dubi irin ladar da ke cikin ’yanta bawa, amma kun ga Annabi (SAW) ya nuna mata ladar zumunci ya fi.
Sadar da zumuncin da iyaye suka kulla
Yana daga manya-manyan ayyukan alheri a Musulunci mutum ya kulla zumunci a kan wanda iyaye suka kulla. Misali, yin abota da dan abokin mahaifinka, ziyartar wadanda yake da zumunci da su.
Abdullahi Bn Umar (RA) yana kan hanyarsa ta zuwa Makkah, wata rana sai ya gamu da wani mutumin kauye ya yi masa sallama, sai ya sauka daga kan jakin da ya hau, ya bai wa mutumin, kuma ya cire rawaninsa ya ba shi. Sai Abdullahi Bn Diinar ya ce: “Ba sai ka ba shi duka ba mutumin kauye ba ya raina kadan. Sai Bn Umar ya ce: “Ai wannan abokin Umar (RA) ne kuma ya ce: “Na ji Annabi (SAW) yana cewa: “Yana daga mafi kyan hali, mutum ya sadar da zumuntar da mahaifinsa yake sadarwa” Muslim.
Malik Bn Rabi’a (RA) ya ce: “Wani mutum ya zo ya ce da Annabi (SAW): “Iyayena sun rasu! Akwai sauran biyayyar da ya wajaba in yi musu? Sai ya ce: Akwai.
(1) Yi musu addu’a. (2) Nema musu gafara. (3) Aiwatar da wasiyyarsu. (4) Sadar da zumuncin da suka kulla. (5) Girmama abokansu.” Abu Dawud.
Hatta sadar da zumuncin matarka da ta rasu, kana iya sadar da shi. Kawar Khadija (RA) takan zo ta gaishe da Annabi (SAW) har gida. Shi kuma yakan yanka rago, ya aika mata da nama. Har wata rana A’isha (RA) ta nuna kishinta a kan haka, sai Annabi (SAW) ya ce: “(Khadija) Ta kasance kaza da kaza (ya yabe ta) kuma ta haifa mini ’ya’ya.” Bukhari/Muslim.
Ku dubi yadda Annabi (SAW) ya kare mutuncin matarsa Khadija bayan rasuwarta, saboda taimaka masa da ta yi a rayuwa da haifa masa ’ya’ya da ta yi. Yau sai ka ga Musulmi yana wulakanta matarsa da suka sha wahala tare, saboda yanzu Allah Ya yi masa arziki, kuma ya auri mata kyawawa ’yan birni.
Ya bayin Allah masu girma! Ku ji tsoron Allah (SWT) ku kyautata zumuncinku, domin yanke zumunci yana zama dalilin tawayar arziki da tsinuwar Allah da shiga wuta.
Allah (SWT) Ya ce: “Ba ku jin tsoron idan kuka juya baya (ga dokokin Allah), ku yi ta aikata barna kuna yanke zumuncinku. Wadannan (masu barna da yanke zumunta) su ne wadanda Allah Ya la’ance su, Ya kurmantar da su, Ya makantar da idanunsu.” (Suratu Muhammad: 22- 23).
Jubair Bn Mud’im (RA) ya ruwaito Annabi (SAW) yana cewa: “Mai yankewa (mai yanke zumunci) ba zai shiga Aljanna ba.” A wata ruwayar “Mai yanke zumunta ba zai shiga Aljanna ba.”
’Yan uwanka na kusa su ne
(1) Wadanda kuka fito ciki daya, uwa daya uba daya, mazansu da matansu.
(2) Wadanda kuke uba daya, uwa daban-daban.
(3) Wadanda uwa ta hada ku, uba kowa da nasa.
(4) Baffa shakiki, wanda suka fito ciki daya da mahaifinka.
(5) Baffa Li-abbi, wanda suka hada uba kawai da mahaifinka.
(6) Dan baffa shakiki
(7) Dan baffa Li-abbi.
Haka dai har zuwa karshen dangi na bangaren uwa da uba duka. Wani ya fi wani kusanci, kusan kamar yadda yake a rabon gado.
Ya ’yan uwa masu girma! Ana so duk abin da ya samu daya daga cikin ’yan uwa, a taru a magance shi gaba daya. Rashin lafiya ne, bashi ne, aure ne, kowa ya bayar da gudunmawarsa.
Akwai wadansu dangogi masu albarka da za su ba ka sha’awa. Duk abin da ya taso wa mutum daya daga cikin dangin, za a sa shi ne a tsakiya. Babba a dangin zai dora wa kowa abinda zai kawo, domin a taru a warware matsalar. Ba a barin mutum da wahalarsa shi kadai. Allah Ya yi musu albarka, Allah Ya ba mu ikon koyi da su.
Akwai wadansu watsatsun dangogi da ba ruwan kowa da kowa. Kowa ta kansa yake yi, babu tattaunawa na dangi, babu taimakekeniya a tsakaninsu. Allah Ya tsare mu da irin halayensu.
Mata ku guji raba zumunci
Akwai matan da ba su kaunar su ga mazansu na taimakon ’yan uwansu.
Akwai wadansu matan kuma da kishi yake sa su raba zumunci a tsakanin ’yan uwa. A mafi yawancin gidajen da ake da mace fiye da daya, ba su barin ’ya’yansu su yi zumunci da ’yan uwansu, wato ’ya’yan kishiyoyinsu, wadanda su ne ’yan uwansu masu matsayi na biyu. ’Yan uwa Li-abbi. Akan kira su ’yan uba, an dauke su abokan gaba maimakon ’yan uwa na zumunci. Sai kowace mace ta tsare ’ya’yanta ta hana su mu’amala da ’yan uwansu, saboda tana kishi da uwarsu. Wadansu matan ma WA’IYAZU-BILLAHI har daukar sunayen ’ya’yansu suke yi su kai wa bokaye a yi musu sihiri ko a sanya ubansu ya kyamace su, ko su kyamaci junansu, ko a tauye musu ci gabansu. Kada uwarsu ta amfana da su, ka ga mace ta haifi ’ya’ya masu yawa, maza da mata amma duk babu mai iya warware mata matsalarta.
Allah (SWT) Ya ce: “…Kuma suna yanke abin da Allah Ya ce su sadar (zumunci) kuma suna aikata barna a bayan kasa. Wadannan su ne masu hasara.” (Suratul Bakara: 27).
Allah Ya daukaka Musulunci da Musulmi Ya kaskantar da kafirci da kafirai. Allah Ya ba mu ikon kyautata zumuntarmu. Allah Ya kara mana zaman lafiya, Ya albarkaci zuriyarmu, Ya bunkasa mana gonakinmu Ya cire wa matasanmu lalaci da kasala, amin!
Imam Abdulmumin Ahmad Khalid
ya aiko da wannan huduba ce daga Msallacin Badar Kubwa, Abuja.