A ranar Alhamis 15 ga Disamba, 2022 Babbar Kotun Musulunci a Jihar Kano take yanke hukunci ga Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, wanda aka gurfanar a gabanta kan zargin batanci ga Annabi Muhammad (SAW).
Aminiya ta yi waiwaye kan wannan dambarwa, wadda ta kai ga mukabala tsakanin Abduljabbar da malaman Kano, dakatar da shi daga gabatar da karatuttttuka, haramta sanya karatuttukansa a kafofin yada labarai da irin wainar da aka toya a shari’arsa a gaban kotun Musulunci.
Ga jerin muhimman abubuwan da suka wakana, a tsawon fiye da shekara guda da ake kai ruwa rana a kan wannan batu.
- Na bai wa lauya N2m ya kai wa alkali don a sake ni —Abduljabbar
- Kotu ta ci Sheikh Abduljabbar tarar Naira miliyan 10
Zargin Abduljabbar da batanci
Za a iya cewa mas’alar Abduljabbar Nasir Kabara ta fara ne tun bayan da wasu malaman Jihar Kano da ke wakiltar akidu daban-daban (Kadiriyya da Tijjaniyya da Izala) suka rubuta wa Gwmnatin Jihar Kano takardar korafi game da abin da suka kira ’yin batanci ga Ananbi Muhamamd Sallahu Alaihi Wasalalm’ da malamim yake yi a cikin karatuttukansa da yake gabatarwa a majalisinsa da ke Masalalchin Ashahabul Kahfi da ke unguwar Gwale da kuma Sabuwar Gandu a jihar.
Har ila yau malaman sun yi kaset guda wanda ya kunshi wasu daga cikin karatuttukan da Malam Abduljabbar din ke gudanarwa a majlisai nasa inda suka mika su ga gwamantin.
Hakan shi ya janyo a ranar 5 ga watan Fabrairu, 2021, Gwmanatin Jihar Kano, bayan samun oda daga kotu, ta bayar da umarnin dakatar da Malam Abduljabbar Kabara daga yin wa’azi tare da rufe masallachinsa na Ashabul Kahfi.
Haka kuma gwamnatin ta hana sanya karatuttukan malamin a kafafen watsa labarai da ke jihar, matakan da ta ce ta dauka ne don ta magance yiyuwar barkewar rigima a jihar.
Mukabalar Abduljabbar da malamai
Sai dai wannan abu bai yi wa Malam Abduljabbar din dadi ba inda ya yi ta kira ga gwamnatin da ta shirya mukabala a tsakaninsa da malaman da ke ganin akwai lam’a a karatuttukan nasa.
A ranar 2 ga Fabrairu, 2021 gwamnatin ta amince da bukatar malamin, musamman da ya rika iraye-kiraye da a yi masa adalci.
A ranar 8 ga watan Yuli sai gwamantin ta sanar cewa za a yi mukabalar a ranar 10 ga watan Yuli za a gudanar da mukabalar a gaban malamai na ciki da wajen Najeriya don zama shaida game da abubuwna da za su faru a wanan lokaci.
Sakamakon mukabala
A ranar 10 ga watan Yuli aka yi mukabalar tsakanin Abduljabbar da malaman na Kano inda bayan an tashi, alkalin mukalbalar, Farfesa Salisu Shehu, ya bayyana cewa Abduljabbar din ya kauce wa tambayoyin da aka yi masa.
Farfesa Salihu Shehu ya bayyana cewa a maimakon ya bayar da amsa a kan tambayar da aka yi masa, sai ya rika korafin cewa ba shi da isasshen lokacin da zai yi bayani.
A nasa bangaren, Abduljabbar ya zargi Gwamnatin Jihar Kano da hana shi isasshen lokacin yin baynai da kuma rashin ba shi bayanai a kan abubuwan da za a yi mukabalar a kansu kafin zuwan ranar.
Maka Abduljabbar a kotu
A ranar 16 ga watan Yuli kuma sai Gwmanatin ta Kano ta gurfanar da malamin a gaban Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu bisa zargin shi da yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW).
A ranar 28 ga watan Yulin 2021, aka gurfanar da Abdujabbar din, inda lauyoyin gwamnati karkashin jagorancin Barista Saida Suraj (SAN) suka nemi a kotun ta dage shari’ar zuwa lokacin da za su kawo maat takardar caji a maimakon takardar kara.
A ranar 18 ga watan Agusta, 2021 kotun ta sake dage shari’ar sakamakon rashin fitowar takardar caji daga bangaren masu gabatar da kara, wanda ya sa lauyoyin malamin karkashin jagorancin Barista Saleh Bakaro suka zargi gwamnati da jan kafa wajen shariar.
Kotu ta sa a duba lafiyar kwakwalwarsa
A ranar 3 ga watan Satumba lokacin da aka karanta wa Abduljabbar Kabara cajin da masu kara suka gabatar inda ya yi gum da bakinsa lamarin da ya janyo kotun ta yi umarnin a gwada kwakwalwarsa da kunnensa a asibiti don sanin matsayin lafiyarsa.
Lokacin da kotun ta zauna a ranar 17 ga watan Satumba an gabatar mata sakamakon gwaje-gwajen kwakwalwa da na kunne da aka yi wa Malam Abduljabbar Kabara, wadanda suka nuna cewa malamin lafiyarsa lau.
Batawar Abduljabbar da lauyoyinsa
Daga nan ne kuma lauyoyinsa suka fice daga shari’ar inda kuma Abduljabbar din ya zarge su da tilas shi kin yin magana a zaman da ya gabata wai don kotu ta ce ba shi da lafiya, wanda hakan zai sanya gwamnati ta kau da kai daga tuhume-tuhumen da take yi masa.
Sai dai a martanin da lauyoyin nasa suka yi ta bakin Barista Rabi’u Muhammad sun musanta zarge-zargen da ya yi musu inda suka yi barazanar maka shi a kotu matukar bai janye kalamansa a kansu ba.
A ranar 2 ga watan Oktoba sabbin lauyoyin Abduljabbar karkashin jagorancin Muhammad Umar sun nemi kotu ta bayar da belin sa, amma kotu ta yi watsi da rokon nasu.
Sauraron shaidu
A ranar 14 ga Oktoba aka fara sauraren shaidun masu kara, inda Abduljabbar Kabara ya zargi sabbin lauyoyinsa da rashin yi wa shaidun masu kara tambayoyin da suka kamata, inda ya nemi a ba shi dama ya yi musu tambayoyin da kansa lamarin da ya haifar da rashin jin dadi daga wajen lauyoyin nasa.
A ranar Oktoba 28 har zuwa ranar aka kai gaba da sauraren shaidun masu kara
Lauyoyinsa sun janye
A ranar 11 ga Nuwamba sababbin lauyoyin Abduljabbar Kabara suka fice daga shari’ar sakamakon rashin samun daidaito a shari’ar lamarin day a janyo tsaiko a wajen ci gaba da sauraren shaidun masu kara.
A ranar 10 ga watan Nuwamba Abduljababr Kabara ya sami sabon lauya, Barista Mohammed O. Ambali (SAN) sai dai ya nemi a ba shi lokaci don yin nazargin shari’ar.
A ranar 24 ga watan Disamba har zuwa wani lokuta aka ci gaba da sauraren shaidun masu kara.
Sake sauraron shaidu
A ranar 2 ga watan Fabrairu, 2022, lauyan nasa Barista Mohammed Ambali, ya nemi kotu da ta dawo da shaidar masu gabatar da kara na farko don sake amsa wasu tambayoyi.
A ranar 17 ga watan shaidar masu gabatar da kara na farko ya dawo gaban kotun kamar yadda aka bukata inda kuma lauyoyin Abduljabbar din suka yi masa tambayoyi.
Sabon lauya sun bata da Abdujabbar
A ranar 10 ga watan Maris kotun ta ci gaba da sauraren shaidun masu gabatar da kara da na uku da na hudu.
A ranar 30 ga Maris lauyoyin Abduljabbar Kabara suka gabatar da kaset a gaban kotu.
A ranar 29 ga watan Afrilu Lauyan Abduljabbar Kabara Barista Mohammed O. A (SAN) shi ma ya fice daga shari’ar inda ya zargi Abduljabbar din da rashin yin biyayya ga shawarwarin lauyoyinsa.
Ya rasa lauyan da zai kare shi
13 ga Mayu, kotu ta nemi Hukumar bayar da Agajin Shari’a ta Kasa (Legal Aid Council) ta ba Abduljabbar lauya saboda ya rasa lauyan da zai kare shi, inda ya zargi bangaren gwamnati da yi wa lauyoyin da ya nemi su yi masa aiki barazanar rasa rayukansu.
A ranar 2 ga watan Yuni Hukumar ‘Legal Aid Council’ ta bayyana wa kotu cewa ba za ta kare Abduljabbar Kabara ba, saboda yana da halin da zai iya daukar lauya da aljihunsa kuma shari’arsa ba ta cikin jerin shari’un da hukumar ke ba wa kariya.
A wannan ranar ne kuma kotun ta umarci barista Dalhatu Shehu Usman da ya zo kotun ya ba Abduljabbar kariya.
A ranar 9 Yuni sabon lauyan Abduljabbar Kabara, Barista Dalhatu Usman, ya fara bayyana a gaban kotun.
A ranar ce aka fara sauraren kaset din karatuttukan Abduljabbar din kuma a ranar kotun ta yi umarni da a ba wa masu gabatar da kara kaset din don yin nazari akai.
Abduljabbar ya kare kansa
A ranar 23 ga watan Yuni Abduljabbar ya fara kare kansa inda kuma lauayoyinsa suka nemi kotu da ta sallame shi kasancewar a ganinsu bai aikata laifin da ake zargin sa da aikatawa ba, bisa hujjar cewa cajin da ake masa ba ya bisa doka.
A cewarsu, cajin yana magana ne a kan yin batanci ga Ananbi Muhamamd Sallallahu Alaihi Wasallam, amma kuma masu gabatar da kara suke magana Abduljabbar din ya yi batanci ga manyan malaman Musulunci, wato Bukhari da Muslim.
Lauyan Abduljabbar ya kaurace wa kotu
A ranar 7 ga watan Yuli lauyoyin gwamnati suka fara yi wa Abduljabbar Kabara tambayoyi a matsayinsa na shaidar kariya.
Daga bisani kuma lauyansa, Barista Dalhatu Usman, ya fice daga kotun cikin fushi inda ya zargi alkalin kotun, Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola da hana malamin damar da ta kamace shi.
Haka kuma ya yi zargin alkalin da karbar umarni daga dan uwan Abduljabbar, wato Shaikh Karibullah Kabara, “wanda aka san ba su ga maciji da juna” game da duk abin da za a gudanar a kotun.
A ranar 21 ga watan Yuli zaman shari’ar bai yiwu ba sakamakon lauyan Abduljababr Barista Dalhatu Usman ya kaurace wa zaman kotun.
Hakan ya sa kotun ta umarce shi da ya bayyana gabanta a zama na gaba kasancewar ita ce ta sanya shi yi wa Abduljabbar aiki don haka ya zama wajibi ya yi wa kotun biyayya.
Malamin ya nemi sauyin kotu
A wanann zama ne kuma Abduljababr ya nemi alkalin kotun da ya mayar da shari’ar zuwa wata kotun duba da irin zargin da suke yi masa na rashin adalci.
Amma alkalin ya ce babu kotun da ta dace ta gudanar da wanan shari’a sai tasa duba saboda ita ce Bababr Kotun Shari’ar Musulunci a Kano, sannan ita ce mafi kusa da gidan gyaran halin da wanda ake kara yake kuma ita ce mafi kusa da mazaunin wanda ake kara.
A ranar 3 ga watan Agusta, lauya Dalhatu ya dawo kotun inda Abduljabbar Kabara ya ci gaba da amsa tambayoyin lauyoyin gwamnati. inda aka rufe wannan babi a wanann zama.
A zaman ne Lauya Dalhatu ya jaddada rokon neman canjin kotun amma lauyoyin gwamanti suka yi suka a kan hakan.
Sai dai alkalin kotun, Ibrahim Sarki Yola, ya shawarci wanda ake kara da ya kai korafinsa gaba a kan rashin adalcin da yake zargin za a yi masa.
A ranar 11 ga watan Agusta lauyoyin gwamanti suka gabatar da jawabi na karshe inda kuma aka nemi bangaren Abduljabbar da ya gabatar da nasa jawabin a zama na gaba.
Reshe ya juye da mujiya
Sai dai a ranar 15 ga watan Satumba Abduljabbar Kabara ta hannun lauyansa, Barista Dalhatu, ya yi karar Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu da Gwamnatin Jihar Kano gaban Bababr Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano.
Sai dai kotun ta umarci masu kara da su je su sake tsara yadda kararsu za ta kasance, saboda sun yi ta ba bisa doka ba.
Abduljabbar da lauyansa sun komar da kararsu gaban wata Babbar Kotun Taryya da ke Abuja inda a zaman kotun na ranar 19 ga watan Satumba, kotun, karkashin jagorancin Mai shari’a Emeka Nwite ta ci tarar Abduljabbar Kabara Niara miliyan 10 saboda shigar da kara iri guda a kotuna biyu masu matsayi iri daya.
Alkalin ya bayyana cewa yin hakan wasa da hankalin kotu ne, sannan ya umarci Lauya Dalhatu Usman da ya biya Gwamnatin Jihar Kano Naira dubu 100.
Dambarwar karbar cin hanci
A ranar 29 ga watan Satumba lauyansa, Barista Dalhatu ya kaurace wa zaman kotun, lamarin da ya sa malamain ya zargie shi da karbar Naira miliyan biyu daga gare shi da sunan zai ba wa alkalin kotun don ya wanke shi.
A lokacin alkalin ya musanta karbar kudin da ake ikrarin an ba shi, inda kuma ya kalubalanci lauya Dalhatu da ya fito ya fadi shaidarsa a kan ya ba shi kudin.
Sai dai a martanin da ya yi, Barista Dalhatu ya musanta zargin da ke yi a matsayin mara tushe ballantana makama.
A ranar ce kuma alkalin kotun ya bayyana cewa an kammala sauraren shari’ar don haka daga baya zai sanar da ranar da kotun za ta yanke hukunci.