✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wai da gaske ne murfin kirjin mutum na iya fadawa?

Wai da gaske ne murfin kirjin mutum na iya fadawa? Kuma idan ya fada ina mafita?  Daga Tasi’u Halliru Maigwanjo   Amsa: E, lallai Mallam…

Wai da gaske ne murfin kirjin mutum na iya fadawa? Kuma idan ya fada ina mafita? 

Daga Tasi’u Halliru Maigwanjo

 

Amsa: E, lallai Mallam Halliru kana bincike tunda ka san murfin kirji. Tabbas akwai murfi a kirji wanda ya raba kirjin da ciki. Shi wannan murfi wani dan nama ne faffada a kasan huhu da yake a shimfide a hade da hakarkari. Tabbas akwai lokutan da wannan murfi zai iya fadawa. Wadannan lokuta kuwa su ne idan an samu hadari kamar na mota ko na harbi ko an caka wuka daidai saitin murfin, ta yadda zai yage ya rufta. Ba za a iya ganewa ba amma sai an yi hoto. Don haka ke nan ruftawar murfin matsala ce da za ta bukaci taimakon gaggawa na ceton rai.

Ni ma nakan ji hakarkarina gefen hagu yana mini zafi kamar ya shige. Ko wannan matsala ce?

Daga S.S. Ma’idawa

Amsa: kwarai kuwa matsala ce. Ai in dai ciwo ne ko zogi mutum yake ji a jikinsa ai ba sai ma an ce masa matsala ba ce, domin shi kansa ya san ba haka yake ba kafin matsalar ta fara. Da fatan za ka samu a je a duba hakarkarin.

Da gaske ne hakora na yin tsatsa?

Daga Sani Umar Malumfashi

Amsa: E, hakora na yin datti mai kama da tsatsa, amma ba tsatsa bane, tunda a kimiyyance tsatsa wato rust, na nuni ne da sinadarai daban da tsatsa ta dattin hakori, wadda ake kira plakue. Tsatsar hakori sinadaran cikinta kwayoyin cuta ne da guntattakin abinci da maiko da sinadarin tartar da sauransu. Idan mutum yana yawan asiwaki ko burushi kuma yana zuwa likitan hakori na kankare masa dattin hakorinsa a kalla sau daya a shekara, da wuya a ga hakoransa sun yi tsatsa.

Wane irin abinci ne ke sa mutum yin tumbi wane ne kuma ba ya sa wa?

Daga Mukhtar Gandu, Kano

Amsa: Ai ko wane irin abinci ne idan kana masa cink eta yanzun nan ne za ka fara ganin kana ajiye tumbi.

Ni ma ina da yawan cin abinci alhali kuma ni ba wani kato bane. Shine nake tambaya yawan ci din ciwo ne ko kaka? Kuma ya za a yin a rage?

Daga Rabi’u Sulaiman

Amsa: E, yawan cin abincin da ya wuce kima – irin wanda kowa ya g aka cinye ya san kana da ci – matsala a likitance, amma ba wai matsala ba ce da za a ce a ciki ko a hanji, a’a matsala ce a tunaninka kai acicin. Don haka daga kwakwalwarka ne, kai za ka zauna ka yi wa kanka fada ka zayyanawa kanka yadda za ka rage yawan sanwarka. Akwai kuma wasu dabaru da za a iya taimaka maka da su, wasu suna da sauki wasu kuma ba sauki. Misalansu sune ta yawan cin abincin da jiki ba ya tsotse shi da wuri, amma masu cika ciki da sauri. Sai ka nemi irin abincin da ka san ‘yan lomomi kadan kake koshi da shi. Mu dai wadanda muka sani sune kamar irinsu nama, wake, doya, gyada, karas, aya, goro, da sauransu, sai kuma na Turawa irinsu kokon oat. Idan ka mai da wadannan irin abinci abincinka a kullum, wata a ce a kalla za ka samu daya daga cikinsu ka ci a kullum, to za ka ga ka rage ci, domin cikinka kullum a cike za ka rika jin sa. 

 Wai yawan shan rake kuwa yana da illa? Domin wasu sukan ce yawan shan rake kamar yawan shan suga ne.

Daga Umar Sarkin Yaki

Amsa: Ai da kana biye da mu da za ka san mu a wannan fili komai idan ya wuce misali mukan iya daukarsa a matsala ko mai iya jawo matsala. Don me ya sa komai ba za mu iya yinsa ko mu ci shi saisa-saisa ba, daidai gwargwado? Ko yawan cin ganye da ‘ya’yan itatuwa da mukan ce a rika yawan amfani da su ai ba dibar kare-mahaukaciya ake nufi ba. Da fatan ka fahimta.

 Ko yawan shan minti yana kawo matsala? 

Daga Sanusi Musa Gusau

Amsa: A’a ba mu da wata masaniya wata matsananciyar illar yawan shan minti. Sai dai mutane da yawa masu sha sukan ce yana sa su saurin jin yunwa.

  Ko ana daukar cutar kuturta daga wanda yake da ciwon?

Daga Amatullah M.

Amsa: A’a in dai mai ciwon ya sha =magungunan kashe kwayar cutar ba wani abu, ba za a dauka ba, ko da kuwa ana ganin irin illar da ciwon ya masa a jiki.

Ni mai aiki ne a cikin kura. A da ba na amfani da takunkumin fuska amma a yanzu ina yi. Duk da haka dai ina ji kamarakwai kurar a kirjina. Mece ce shawara?

Daga Ya’u M. Kankia

Amsa: Ka samu ka ware rana guda domin ka je babban asibiti cikin birni a maka gwaje-gwaje da hotunan kirji a ga ko akwai wani abu a kirjin, domin wata kila asibitinku a nan Kankia za a iya samun karancin kayan aiki.

Wai maganin hawan jini zai iya kawo ciwon suga, na suga kuma zai iya kawo hawan jini? 

Daga Adam Ahmad, Kontagora

Amsa: Ba a cika gani ba a magungunan ciwon suga. Hasali ma magungunan ciwon suga za su iya kiyaye aukuwar hawan jini tunda sukan rage kiba. A magungunan hawan jini kuma a iya cewa e, a wani bincike guda biyu da aka gudanar akwai wani maganin hawan jini kwaya daya da aka tabbatar zai iya toshe aikin sinadarin insulin ya kawo ciwon suga. 

Idan mutum na da hawan jini kuma yana karbar magunguna zai iya tambayar likitansa ko akwai wanda zai iya sa masa ciwon suga (musamman idan akwai tarihin ciwon suga a danginsa) domin a canza masa.