Alhamdulillah da Allah ya kawo mu karshen zabubbukan 2015, wadanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watoINEC ta gudanar a kusan dukkan sassan kasa don zaben shugaban kasa da `yan Majalisun Dokoki na kasa a ranar 28 ga watan Maris da ya gabata da kuma na ranar 11 ga wannan watan na Afrilu, da shi kuma aka yi zaben Gwamnonin jihohi 29, in banda a jihohin Anambra da Kogi da Ekiti da Bayelsa daOsun da Edo da Ondo da na dukkan `yan Majalisun Dokokin jihohi 36. Ko ba komai irin fargabar da aka rika samu na za a yi tashe-tashen hankula da zubar da jini, kai har ma da barazanar za a yi yaki, da `yan kabilar Ijaw ta shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan suka rika yi, muddin dansu bai ci zaben ba, amma sai ga shi cikin ikon Allah an kammala zabubbukan, ba tare da an samu wata mummunar tarzomar da ta game kasa ba, kamar yadda aka samu a zabubbukan shekarar 2011.
Koda yake alkalumman da shugaban hukumar kare hakkin dan Adam Farfesa Chidi Odinkalu ya fitar, sun tabbatar da cewa mutane 55, suka rasa rayukansu a cikin zabubbukan Gwamnoni da na `yan Majalisun Dokin jihohi. Ya ce duka-duka kimamin mutane 200, suka rasa rayukansu a zabubbukan bana,sabanin na shekarar 2011, da mutane 1,000, suka mutu a tarzomar zabubbukan wancan lokaci. Farfesa Odinkalu ya kuma fadi cewa lalle a wannan karon, sai mutanen kasar nan su kara gode wa Allah da wannan nasara da aka samu idan an yi la`akari da irin yadda aka rika zargin an tara dinbin makamai don yin amfani da su a lokacin zabubbukan da hasashen barkewar munanan rigingimu da mutanen cikin gida da na waje suka rika yi wa kasar nan, a wannan zaben. Don haka sai godiya.
Ba ma wannan ba, irin canjin da aka samu cikin ruwan sanyi a karon farko a cikin tarihin wannan dimokuradiyyar ta hudu da yanzu aka samu shekaru 16, ba kakkautawa jam`iyyar PDP tana mulki, in banda a wannan karon da jam`iyyar adawa ta APC za ta karbi mulkin gwamnatin tsakiya,sannan kuma ta samu rinjaye a Majalisun Dokoki na kasa da kuma gwamnonin jihohi da Majalisun Dokokinsu. A jihohi irin su Kaduna da jiha ta Katsina da Jigawa da Kano da Sakkwato da makamantansu rahotanni sun tabbatar da cewajam`iyyar APC ita kadai za ta yi kidanta ta yi rawarta a cikin tafiyar da mulkin irin wadancan jihohi.Wato ma`ana ita ta ci Gwamnan jiha, ita kuma ta lashe dukkan kujerun Majalisun Dokokin jihar. Haka labarin yake a wasu jihohi Kudancin kasar nan musamman na Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas. Irin wannan tuwona,maina da aka samu a cikin zabubbukan,abubuwan da ke sa fargaba a zukatan `yan kasa ne cewa lami za a yi wannan mulkin.Ma`ana ba wata kakkarfar adawa da za a samu, bare a samu wasu ayyukan raya kasa.
Idan wannan abin a duba ne, ni babban abin da ya fi damuna shi ne irin sabon salon canja shekar da akai ta samu daga jihohi daban-daban na kasar nan bayan zaben shugaban kasa da ya bai wa dan takarar jam`iyyar adawa ta APC, Janar Muhammadu Buhari nasara. A cikin kasa da kwanaki goma da yin zaben kafin a zo yin na Gwamnonin jihohi an samu wasu manyan jiga-jigai da dubun -dubatar magoya bayan jam`iyyar PDP da suka yi ta canjin sheka zuwa jam`iyyar APC. Alal misali a jihar Edo da APC take mulki, da rana tsaka jami`in daidaito na yakin neman zaben shugaba Jonathan Mista Charles Airhiabere da wasu magoya bayan jam`iyyar PDP 10,000, a jihar suka koma APC. A jihar Gwambe, inda PDP take mulki, Alhaji Ibrahim Zamfara dan Kwamitin Dattawan jam`iyyar da shugaban masu rinjaye a Majalisar Dokokin jihar Alhaji Mamman Alkali da wasu mataimaka na musamman na gwamnan jihar, 50, su ma sun koma jam`iyyar ta APC.
A can jihar Kebbi, inda yanzu APC za ta karbi mulki, jiga-jigan jam`iyyar PDP irin su Alhaji Nasir Musa Shehu da Alhaji Zubairu Turaki da Alhaji Hussain Adamu da wasu magoya bayan jam`iyyar ta PDP su kimanin 43,00, suka canza sheka zuwa APC, ana kwanaki 4, zuwa 5, a tafi zabubbukan Gwamnoni da na `yan Majalisun Dokokin jihohi. A jihar Jigawa inda nan ma Jam`iyyar PDP take mulki, mutane irin su tsohon Gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Saminu Turaki da mataimakin Gwamna mai ci yanzu Alhaji Ahmed Muhammad Gumel da Sanata Muhammadu Dudu da Sanata Muhammad Alkali da daruruwan magoya bayansu suka kaurace wa PDP zuwa jam`iyyar APC. Haka irin wannan labarin yake na kaurace wa PDP zuwa APC a jihohi irin su Ribas da Kwara da Nassarawa,duk a zaman guguwar APC ta kada.
Abinka da siyasa da ake son karin jama`a, ba ragi ba. An yi ta bukukuwa a irin wadancan jihohi don karbar masu canza shekar,duk kuwa da an san wasu sun zama mushen gizaka. Don kuwa kadawar guguwar canji ta Janar Buhari a wannan karon ba wani mutum daya da koda Gwamna ne a jiharsa, da zai ce don darajar kansa jama`a suka zabe shi ko sauran `yan takarar da ya tsayar. Amma yanzu idan komai ya nutsa, za ka ji cewa irin wadancan mutane da akan yi wa lakabi da uwarsu ba ta mutuwa a harkokin siyasar kasar nan, su za ka ga sun tare a gindin sabon Shugaban kasa da Gwamnoni, su rika kai kawo ta yadda kafin a ankara sun zama `yan dole a yi da mu, bako sai ya fi dan gida mike kafa ke nan.
Irin wadannan mutane su ne a siyasa akan kira su da sunaye kamar haka:- `Yan shan kai, ko `yan tayi dadi da makamantan sunaye. Da alama Gwamnan jihar Neja bai ji dadin waccan kauracewa ba da ake yi wa jam`iyyarsu, don haka yake bayyana irin wadancan mutane da `Yan siyasar ciki ne kawai. A can ma jam`iyyar APC wanda take samun karuwar, da alama shugabanjam`iyyar na kasa baki daya Cif John Oyegun ba ya murna da canjin shekar tasu, bare ya yi masu maraba, don kuwa an ruwaito shi yana cewa kamata ya yi irin wadancan mutane su hakura su zauna a cikin jam`iyyunsu na asali, ta yadda za su iya karfafa adawa a cikin tafiyar wannan dimokuradiyyar, amma ba kowa ya tare cikin jam`iyya mai mulki ba.
Duk da ya ke a duniya baki daya, ba inda aka ja layin kar wani ya bar jam`iyyarsa zuwa wata, don batu ne na `yancin haduwa da tafiya ta masu ra`ayi ko neman biyan bukata iri daya, da ba don haka ba, da sai in ce a yi dokar da za ta hana `yan siyasa canjin sheka, don kuwa masu yin haka ba masu kawo dauki ba ne, `yan shan kai ne.