✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wacce ta fi kowa tsawon farata a duniya ta yanke su

Kundin tarihi na duniya da ake kira Guinness World Record ya karrama Ayanna Williams sakamakon barin faratanta wadanda suka fi na kowa tsayi a duniya…

Kundin tarihi na duniya da ake kira Guinness World Record ya karrama Ayanna Williams sakamakon barin faratanta wadanda suka fi na kowa tsayi a duniya har kusan zuwa shekara 30 ba tare da yanke su ba.

Ayanna Williams wacce take alfahari bayan karramawar Guinness World Record da ta samu saboda tsawan faratan, an gwada tsayinsu ya bada tawon sentimita 733.55.

A yanzu da ta yanke shawarar yanke su, amma duk da haka ta ce, “Har yanzu nice sarauniyar farata, duk da rashinsu da zan yi.

 Ayanna Williams ta bar faratan nata sun  yi tsayin har zuwa shekara 30 ba tare da yanke su ba kuma hakan bai hana ta gudanar da wasu aiyukanta ba na yau da kullum, kamar wanke tufafi da sauya shimfixar kwanciya.

Lokaci guda Ayanna ta yanke shawarar sauya rayuwa ta hanyar yanke faratan, don gudanar da wasu harkokin yau da gobe fiye da na baya, sai dai tana jimamn rashin faratan da ta saba da su, na tsawan lokaci.

Faratan Ayanna
da Kamfanin Ripley na abubuwan al’ajabi suka dauki hoto
Ayanna
Hoton da Kamfanin Ripley na abubuwan al’ajabi suka dauketa

A yayin da Ayanna take ganawa da Guinness ta ce: “Ina ta dawainiya da faratana na tsawan shekaru amma yanzu ina shirin shiga sabuwar rayuwa.

“Na san yanzu zan yi kewarsu, amma sai dai na wani lokaci ne kuma lokaci ne yayi da za a cire su.

“A duk lokacin da nake gudanar da harkoki na sai na kasance mai kula sosai.

“A raina na shirya matakai daban-daban don kar na jiwa kaina ciwo da faratan kuma nayi sanadin karya su kuma a yanzu ina murnar yanke su da kaina saboda shirin shiga sabuwar rayuwa.

“Idan na bar faratan ko kuma na yanke su, zan ci gaba da kasancewa sarauniyar farata, ba faratan bane ke sarrafa kansu ba, ni ke sarrafa su.”

Kafin yanke faratan, mahaifiyar kakar Ayanna tana samar da kwalabe uku zuwa hudu na man goge faratan sannan a yi masu fenti, kafin sauya launinsu yana daukan wasu kwanaki.

Duk da farata sun kasance wa Ayanna amintacciyar halitta, hakan bai hana ta yanke shawarar yanke su ba, kuma ba tada niyyar sake barin faratan nan gaba.

Ayanna ta samu karramawar Kundin tarihi na duniya a shekarar 2017 bayan ta karbi kambun daga Lee Redmond wacce ta kasance mafi  tsayin farata a duniya a tarihi.

Ayanna wacce ta fito daga Jihar Texas ta kasar Amurka, ta fara tara faratan ne tun a shekarar 1979.

Ta kasance tana sanya faratan a cikin man zaitun mai dumi kullum ta hanyar amfani da kwalba don kara masu karfi da kuma goge su don su kasance cikin yanayi mai kyau.

Ta ce: “Wannan wani kalubale ne ga ni kaina, don naga yadda faratan za su girma kafin su fara nannadewa da sauya fasalinsu.

“Na dade ina sanya ranar da zan yanke faratan, amma ban yi ba kuma abin mamaki ne yadda suka zama wani bangare na jikina.

“Ina tunanin faratana za su iya gabatar da ni ga jama’a da dama, na shahara ne da suna mace mai farata, amma sai dai nayi ta masu bayanin wasu abubuwan game da ni.”