✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wa ke son Gwamna Suntai na Jihar Taraba ya mutu?

Daya-da-daya ba babban labarin da kafofin yada labarai na ciki da wajen kasar nan suka ci kasuwarsa a `yan kwanakinnan irin labarin dawowar Gwamnan Jihar…

Daya-da-daya ba babban labarin da kafofin yada labarai na ciki da wajen kasar nan suka ci kasuwarsa a `yan kwanakinnan irin labarin dawowar Gwamnan Jihar Taraba, Mista danbaba danfulani Suntai daga jinyar watanni 10 da ya yi a kasashen Jamus da Amurka, tun daga ranar  27 ga watan OKtobar bara zuwa 25 ga watan Agustan da ya gabata.
 An garzaya da gwamna Suntai ne zuwa kasar Jamus kwanaki biyu, bayan ya samu hadarin jirgin sama, a wani karamin jirgin samasa da shi da kansa yake tukawa kusa da Yola babban birnin jihar Adamawa a ranar 25 ga watan Oktoban barar. Bayan ya samu watanni biyar yana jiyya a Jamus din ne, aka kuma wuce dashi kasar Amurka a watan Maris din da ya gabata a dai ci gaba da neman magani. Jiyyar da akai ta shaci fadi akan makomar gwamna Suntai, koda bayan ya warke akwai zargin kwakwalwarsa ta tabu, kuma ta har abada, don haka koda ya warke zai yi wuya ya iya mulkin jiharsa.
 A gefe daya, baya ga irin na kusa da Gwamna Sunti da mukarraban gwamnatin tarayya da na gwamnatin Jihar ta Taraba a karkashin jagorancin Mukaddashin Gwamnan jihar, Alhaji Garba Umar da bayan makonni uku da yin hadarin gwamna Suntai, Majalisar Dokokin jihar ta yi amfani da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar nan na shekarar 1999, ta zartar da kudirin da ya ba shi ikon rike mulkin jihar har ranar da Allah Ya sa gwamna Suntai ya samu cikakkiyar lafiya ya dawo kan kujjerarsa, sun ta kai wa gGwamnan Suntai ziyarar dubiya. Ita kanta jam`iyyar Gwamna Suntai ta PDP ta kasa baki daya sai da ta tura nata ayarin a karkashin shugabancin Sanata  Hope Uzodinma, kwamitin da tunda ya dawo jam`iyyar ta PDP ba tace da kowa uffan ba, akan sakamakon abin da ayarin ya gano ba, akan matsayin rashin lafiyar gwamnan na Taraba ba, bare kuma ta ce ga mafita.
 A cikin tafiyar da mulki, Mukaddashin Gwamna Alhaji Garba, ya cire Sakataren gwamnatin jihar da wasu Kwamishinoni da ya gada daga Gwamna Suntai, bayan Majalisar Dokokin jihar ta same su da laifin yin sama da fadi da kudin taimakon ambaliyar ruwa na bara. Kazalika Majalisar Dokokin jihar ta yi nasarar tsige Kakakinta. Ga magoya bayan Gwamna Suntai, wadancan matakai da Mukaddashin Gwamna Alhaji Garba ya fara dauka, su suka fara wai nuna masu cewar Mukaddashin gwamnan yana son ya mike kafa, ya gaje kujerar mulki, duk kuwa da ya shaida wa mutanen jihar cewa abubuwan da jami`an gwamnatin suka aikata, koda Gwamna Suntai na kan karagar mulki ba zai barsu ba.
Duk da gwamnatin Jihar Taraba ta ci gaba da biyan kudin jinyar Gwamna Suntai da kuma kula da iyalensa gwargwadon zarafi, wannan bai hana samun rarrabuwar kawunan mutanen jihar ba, akan abin da ya jibanci magoya baya, wato wasu suka zama na mukaddashin gwamnan wasu kuma na Gwamna Suntai, abin takaicin shi ne irin yadda wasu suke yi akan bambancin addini, alhali sun sa ni Jihar Taraba, jiha ce da take wake da shinkafa akan batun addini, ta yadda kusan da wuya ka samu iyalin da suke zalla musulmi ko zalla kirista.
Waccan baraka ta fara fadada a lokacin da Gwamna Suntai ya sauka a Abuja, inda ta tabbata a idanun duniya cewa bai warke ba, don kuwa wani ya riko a kugu aka sauko da shi, haka kuma bisa ga al`ada musamman ga dan siyasa, kamata ya yi a ce Suntai ya gana da manema labarai walau a Abuja ko a Jalingo, babban birnin jiharsa don ya tabbatar wa jama`a ya warke, amma hakan ba ta samu ba. Da ya isa Jalingon ma uwargidansa Hauwa Suntai ta hana kowa ya ganshi, hatta gwamnan jihar Adamawa da ya kwashi karfaffan ayari da kyar da jibin goshi ya samu ganin Gwamnan Suntai, sauran mukarraban gwamnatin jihar da suka hada da mukaddashin gwmnan jihar  da masu fada aji,`duk garkuwa aka yi masu tsakaninsu da ganin Gwamna Suntai,  bare su iya tantance lafiyarsa.
Hatta `yan Majalisar Dokokin jihar nan 16 da suke karkashin jagrancin Kakakin Majalisa Haruna Tsokwa sai da suka yiwa Uwargidan Suntai barazanar za su fara shirin tsige shi kan  ta bari suka gana da shi, ganawar da ta ba su dama suka rusa dukkan ayyukan da Gwamna Suntai ya yi tunda ya dawo jihar, kamar cewar ya dawo bakin aiki bisa ga takardar da ya aikawa Majalisar da rushe Majalisar zartaswar jihar sannan suka shawarce sa da ya koma neman magani, har zuwa lokacin da Allah Ya bashi lafiya.
A gefe daya sauran `yan Majalisar Dokokin jihar 8, a karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye da Uwargdan Gwamna Suntai da gwamnonin jihohin Binuwai da Filato kusan suke kan gaba wajen cewa gwamna Suntai yana cikin koshin lafiya da zai koma bakin aikinsa. Mutane irinsu Farfesa Jerry Gana da Mista John Dara da makamantansu, bisa ga dalilin da suka barwa kansu sa ni, su suka fara bada shelar gwamna Suntai ya warke a lokacin da suka taresa a filin jirgin saman Abuja, har suna masu karawa da cewa da zarar ya isa Jalingo zai iya komawa bakin aikinsa, alhali sun sa ni daga irin yadda suka ga gwamna Suntai, ba Suntai din da kafin ya yi hadari bane.
Ni ina ga daga irin yadda kasar nan ta shiga rudani akan rashin lafiyar tsihon shugaban kasa, Alhaji Umaru Musa `Yar`aduwa, rashin lafiyar da ta zama ajalinsa a watan Mayun 2010, ta isa ishara ga masu shaidar zur don kawai amfanin da zasu samu daga mai mulki da kuma su iyalan mai mulkin akan su shiga taitayinsu, su kuma ji tsoron Allah su daina shaidar zur. Shawara ga Uwrgidan gwamna ba ta wuce ta karbi shawarar `yan Malalisar Dokokin jihar ta a mayar da maigidanta asibiti don ci gaba da neman magani. Ya kamata ta kwan da sanin cewa yau mijinta na faduwa ya mutu ba ta kara jin duriyar irin wadancan mutane, wani mai mulkin za su runguma, ita kuma su bar `ya`yanta da maraici, don haka ta yi hatta da masu son mutuwar mijinta.