✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wa ke neman dusashe hasken tauraruwar Injiniya Ibrahim Gusau?

A wannan makon, mun samu wannan tsokaci ne daga Bilya Umar Gusau, Gida Mai lamba 42, Titin Musa dan Bakura, Unguwar Gwaza, Gusau, Jihar Zamfara;…

 Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar Gwamnan Jihar ZamfaraA wannan makon, mun samu wannan tsokaci ne daga Bilya Umar Gusau, Gida Mai lamba 42, Titin Musa dan Bakura, Unguwar Gwaza, Gusau, Jihar Zamfara; wanda ya bi kadin yadda adawar siyasa ta dauki wasu har suka fara nuna ta’addanci ga wani babban dan siyasa, da ke tare da talakawa. Ga abin da tsokacin nasa ya kunsa:
Hakika muhimmin ci gaba ga kowane dan siyasa da siyasarsa, shi ne ya samu karbuwa daga al’ummarsa da kuma irin ci gaban da ya kawo musu, musamman wajen bunkasa rayuwarsu da kuma samar musu da ababen more rayuwa.
Injinya Ibrahim Shehu Gusau, mutum ne da ya yi suna tun kafin shiga siyasa wajen taimaka wa al’umma da samar musu da ababen amfani na ci gabansu. Wannan kuwa ya samo tushe ne daga ayyukan taimako da tallafa wa jama’a da mahaifinsa, marigayi Alhaji Shehu Bakauye yake yi a lokacin da rayuwarsa.
Ba shakka, tun lokacin da aka zabe shi don wakiltar al’ummar kananan hukumomin Gusau da Tsafe a Jihar Zamfara a Majalisar Tarayya, Injiniya Ibrahim Shehu Gusau ya nuna irin matsayinsa na mutum mai tallafa wa al’ummar mazabarsa, jiharsa da kuma kasarsa ba tare da la’akari da wace jam’iyya mutum ya fito ba; mussaman idan aka lura da irin ayyukan raya kasa da ci gaban al’umma da ya janyo cikin shekaru biyu na wakilci ga mazabarsa.
Ayyukan ci gaban kasa da ya dauki nauyin aiwatarwa da kansa ko kuma ya yi sanadiyyar aka samar da su ta hanyar tuntuba da kuma janyo hukumomin gwamnati a ciki suna da yawa.
Kasancewarsa kwararren Injiniyan kere-kere da sadarwa, da ya san ciki da wajen lamarin ayyukan raya kasa da ci gabanta, ya taimaka sosai ga sanin inganci da gyara ga ayyukan sadarwa da kuma bunkasa ayyukan kimiyyar fasaha na zamani a kusan duk lungu da sako na jiharsa.
Tun lokacin zabensa, ya mayar da hankalinsa ga abin da ya shafi bunkasa ilimin Islamiyya wajen ginawa da bunkasa makarantun Islamiyya na cikin gari da kuma yankunan karkarar Gusau da Tsafe.
Ya dauki nauyin gyara da fadada babbar makarantar Islamiya ta Zawiyya a Gusau. Haka ya gina dakunan kwanciya na zamani da kuma cibiyar shan magani ga dalibai, inda ya taimaka wajen ba fiye da yara 5,000 dama ta fannin inganta karatunsu.
Sai kuma kamfanin samar da kwanon rufi da zayyane-zayyane irin na zamani, GIL na farko irinsa da ya kafa a garin Gusau, domin inganta hanyoyin kasuwanci da daukar ma’aikata. Ya janyo bunkasar tattalin arziki, magance rashin aiki, bunkasa ci gaban masana’antu ga babban birnin Jihar Zamfara da yankin Arewa maso Yamma baki daya.
Baya ga haka, ya bude wata gidauniya ta musamman a kan ilimi, wadda za ta rika tallafa wa ’ya’yan talakawa da marasa galihu wajen biyan kudin makaranta, samar da littattafai da nemo musu guraben karatu domin magance matsalar rashin karatu a tsakanin matasan yankinsa. Tsarinsa na tallafa wa al’umma bai-daya ta hanyar samar musu da ababen taimaka wa rayuwarsu cikin sauki, ya sanya mutane da yawa na ganinsa a yau bisa matsayin mujaddadin gyara da sake tayar da komadar siyasar ci gaba a Jihar Zamfara.
Injiniya Gusau ya shiga kusan kowane lungu da sako na karkarar da ke mazabarsa a lokacin yekuwar neman zabe, don haka bayan zabensu a 2011, ya san kusan duk abin da jama’a suke bukata.
Wadanan matsalolin kuwa sun kunshi matsalar ruwa, hanya, ilimi, takin zamani da kuma sana’o’i. Ganin haka ne ya sanya ya fito da tsare-tsare na ba mazabu tallafi iri daban-daban, wadanda a cikin wata 18 ya samar da rijiyoyin burtsatse masu yawa, famfunan noman rani, injunan tuka-tuka da kuma rijiyoyin kwakware tare da isasshen takin zamani domin tallafa wa manoma.
Haka ma ya rarraba babura, domin amfanin al’ummarsa, ya raba motoci da kekuna tare da tallafa wa limamai da ladanai na masalatai masu yawa domin saukake ayyukan ibada da bunkasa bautar Allah a yankunansu.
Wannan da sauran ayyukan gyara hanyoyin mota da tallafa wa makarantu da littattafai da shirya kacici-kacici a kan muhimman darussan Turanci, Lissafi, Kimiyya da kuma Islamiyya sun taimaka ga ciyar da al’umma gaba kai tsaye a yankin Gusau da Tsafe.
Watakila sakamkon wadannan ayyukan alheri ne da cudanya da al’umma a duk lokacin da ya zo Gusau ko Tsafe ya sanya kusan jama’a suka raja’a da neman wannan talikin ya fito ya nemi kujerar Gwamnan Jihar Zamfara a lokacin da jihar take fuskantar mummunan yanayi ga rashin alkibla da jagoranci ga wadanda ya dace su tallafa wa jama’a.
Rashin tausayi ga al’umma, fuskantar matsalar tsaro da kuma tashe-tashen hankula suna cikin ababen da mafi rinjayen al’ummar Jihar Zamfara suke fuskanta a yanzu, abin da ya sanya suka nemi Injinya Gusau ya dawo Zamfara a shekarar 2015 domin ciyar da su gaba da ceto su daga wannan yanayi.
Yau a Jihar Zamfara, Injinya Ibrahim ya kasance abin tsoro da fargaba ga wasu daga cikin marasa kishin al’umma da ci gabansu dangane da wadannan halayen nasa. Domin haka ma jama’a suke bayyana farmakin da aka kai masa da cewa wata kiyyaya da hassada ne ganin yadda tauraruwarsa take daukaka da samun karbuwa da amincewar mafi rinjayen masu ruwa da tsaki a siyasar Jihar Zamfara.
Shi aikin alheri, hakika ba ya boyuwa kuma yana sanya kusanci ga jama’a. Domin haka ne ake ganin wadannan ayyukan alherin da Injinya Ibrahim yake aikatawa tamkar gado ne daga mahaifinsa, marigayi Alhaji Shehu Bakuye ya dauko.
Ya kasance mai son amfani da dukiyarsa wajen daukaka abin da zai amfani al’umma ko a gida ko a waje, maimakon yawan gine-gine ko sayen dankara-dankaran motoci na alfarma.
Tsawon hawansa bisa wannan kujerar ta wakilci a majalisa, ya maida hanklai ga abin da zai taimaki al’ummarsa da kuma ba su damar bunkasa yankunansu.
kokarinsa na kawo koyarwa ta ilimin kimiyya da fasaha da amfanin da kwamfuta ga wasu daga cikin makarantu tare da bude cibiyar koyar da ilimin sadarwar zamani da amfani da na’urorin kwamfuta, ya taimaka wa daruruwan matasa a wurare daban-daban.
Ya fito ya nuna cewr ba tara dukiya ne a gabansa ba, kasancewar yana da kwarewa da iya aiki a mukaman da ya rike a baya, abin da yake damunsa shi ne hanyar da za a fito da al’umma daga halin da suka shiga sakamakon sakaci da rashin iya jagoranci na wasu ’yan siyasa.
Sau da yawa, a zauren Majalisar Tarayya, yana nuna bukatar samar da kulawa ta musamman ga lamarin da ya shafi Arewa da ’yan Arewa, mussaman matasa da ke fama da rashin aikin yi. Ya taimaka musu ga cin ma wannan buri a wasu bangarori da yawa.
Ba shakka wadanda suka dauki nauyin ’yan bangar siyasa domin kai wannan farmaki gare shi, sun yi ne da biyu, ko domin neman dushe tauraruwarsa da ke haskakawa ko kuma adawa ce ta yi musu yawa suke neman rufe bakinsa.
’Yan bangar siyasa, dauke da miyagun makamai dai sun far masa a lokacin da yake kokarin halartar taron sulhuntawa dangane da matsalolin jam’iyya a masaukin Shugaban kasa, da ke cikin garin Gusau.
Sakamakon wannan harin wanda cikin ikon Allah Ya samu kubuta daga sharri da aniyar mugaye, an kona daya daga cikin motocinsa, aka kuma kwashe masa dimbin kudi, aka kuma yi wa wasu magoya bayansa raunuka.
Kusan duk wanda ya san Injiniya Ibrahim, ya san mutum ne mai son zaman lafiya. Ba ya tafiya da ’yan banga, ba ruwansa da yawo da masu kiyaye lafiyarsa, domin kuwa yana ganin ya wadatu da hakan bisa ga kasancewar gida yake kuma cikin aminci. Watakila a sakamakon sanin haka ne ya sanya ’yan bangar, wadanda aka dauko haya daga wasu wurare suka samu cin karensu ba babbaka kafin mutanen gari su kawo masa agaji.
Ba shakka masu daukar nauyin irin wannan ta’asar, ya dace su gane cewa, ba wani abin da mutum zai cim mawa idan ya ci mutuncin dan uwansa, baya ga lalaci da kuma karin asara a rayuwa. Allah Ya kiyaye, amin.