Daga Hussein Yahaya
Cibiyar Binciken Kayan Lambu ta Ƙasa (NIHORT) ta gano wani ƙwayar cutar virus dake addabar gonakin kuɓewa a faɗin ƙasar nan.
Hukumar gudanarwar NIHORT ta ce manoman kuɓewa sun koka kan yadda virus .ɗin ke lalata kusan 70% na duk gonar da ya kama.
Ta ce ta samu rahotannin ɓarkewar cutar daga jihohin Oyo, Ogun, Osun, Ondo, Ekiti, Lagos da Niger.
‘Kasuwancin kubewa akwai riba sosai’
Tsadar Tumatir: An koma miya da yalo a Abuja
Kuma bayan da jami’anta suka bincika sai suka gano cewa virus ne ke haddasa cutar.
Hukumar NIHORT ta ce alamun virus ɗin sun haɗa da fitowar wani ƙullutu a ƙarƙashin ganyen kuɓewar kafin daga bisani ya fara nannaɗewa tare da sauya launi zuwa rawaya.
NIHORT ta kuma shawarci manoma su ci gaba da yi wa gonakin kuɓewarsu feshin maganin ƙwari duk mako da zarar sun ga alamun virus ɗin.
Sannan kuma hukumar ta ce ta duƙufa wurin bincike domin samar da gamsasshen maganin da zai kashe virus ɗin nan take.