“Inda ranka” in ji masu iya magana. “Ka sha kallo”. Domin yadda aka san soyayyar uwa da danta za a yi mamaki a ji ta cutar da shi, amma hakan ta faru a Kalaba, inda wata mata ta sheka wa danta tafasasshen ruwan zafi ya kone sosai.
Matar mai suna Maryam Zakari wacce aka fi sani da Asabe ta kona matashin dan cikinta da ta haifa mai suna Babanne Abdullahi da suke zaune tare a Unguwar Hausawa da ke Kalaba, Babban Birnin Jihar Kuros Riba a bisa zarginsa da neman mata wanda hakan ta sa ya daina ba ta ’yan kudin da yake samu daga sana’ar da yake yi ta leburanci.
Matashin da kaninsa na aikin leburanci ne a Kasuwar Manja domin su samu abin da za su rufa wa kai asiri su kuma taimaka wa mahaifiyarsu, amma suna wannan aikin ne kaninsa ya zargi wan nasa Babanne da neman mata saboda rashin kai kudin da ya samu gida wurin mahaifiyarsu.
A hirar da wakilinmu ya yi da wasu shaidun gani da ido, sun ce mahafiyar tasu ta je ta sheka wa dan nata ruwan zafi ne cikin fushi kuma domin ta ladabtar da shi.
“Ruwan zafi tafasasshe ta kwarawa wa dan nata yana daki kwance, inda ya yi masa mummunar kuna tun daga mararsa har zuwa mazakutarsa, sauran jikinsa kuma duk ya sabule fatar jikinsa.
“Ko da abin ya faru mijin da take aure mai suna Zakari ya buga wa wani amininsa waya kan ya zo ya ga abin da matarsa ta aikata.
“Nan take aka dauki matashin zuwa wani asibiti mai zaman kansa da ke Unguwar Hausawa.
“Ganin haka kuma ta sa mutane suka yi ca a kan Asabe tun daga gidan har asibiti suna neman su dauki doka a hannu amma aka hana.”
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Zakari miji ga matar amma ya ce shi ba zai iya cewa komai ba a yanzu, har sai an ceto rayuwar matashin.
Ita kuma Maryam uwar yaro an boye ta gudun kar fusatattun matasan su far mata su kuma hallaka ta. Maryam ’yar asalin Jihar Jigawa ce daga garin Dutse, yayin da mijinta mai suna Abdullahi Miga shi ma daga Jigawan yake daga garin Miga.
Wannan abu mai kamar almara ya ba wa mazauna garin mamaki matuka, musamman al’ummar Hausawa.
Kan haka ne wakilinmu ya tuntubi wata matar aure mai suna Zuwaira Umar shin ko matakin ladabtarwar da uwar matashin ta dauka shi zai magance matsalar da ake son gyarawa?
Matar da amsa da cewa, “A’a, addu’a ta iyaye ce mafita, domin addu’ar iyaye karbabbiya ce don haka zai fi dacewa iyaye su dage da yi wa ’ya’yansu addu’a maimakon kurari da nuna bacin rai.
“Kamata ya yi ta fi mayar da hankali wajen yin addu’a don yaran yanzu sai a hankali duka ko zagi da wasu iyaye ke yi wa ’ya’yansu a maimakon su nutsu kara sanya wa yake su kangare,” inji ta.
Wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kuros Riba SP Irene Ugbo dangane da labarin, inda ta ce babu wani abu mai kamar haka da rundunar ta samu labari.