✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Usain Bolt ya yi ritaya daga buga kwallon kafa

Shahararren dan tseren duniya kuma dan asalin Jamaica Usain Bolt a shekaranjiya Laraba ya sanar da daina buga wasan kwallon kafa bayan ya yi wasanni…

Shahararren dan tseren duniya kuma dan asalin Jamaica Usain Bolt a shekaranjiya Laraba ya sanar da daina buga wasan kwallon kafa bayan ya yi wasanni biyu kacal a kulob din Central Coast Mariners da ke Australiya.

Bolt wanda ya yi wasannin gwaji a kulob da dama ciki har da na Borussia Dortmund da ke Jamus, a watan Oktoban 2018 ne ya koma kulob din Central Coast Mariners a matsayin gwaji.  Bayan ya yi wasanni biyu a kulob din inda ya samu nasarar zura kwallaye biyu a raga a wasannin sada zumunta  sai ya nemi su kulla yarjejeniyar da kulob din amma abin ya ci tura saboda matsalar yawan albashin da kulob din ya ce zai rika biyansa.  Daga nan ne kulob din Balletta da ke Malta ya yi zawarcinsa amma Bolt ya ce su kai kasuwa.

Tun daga wancan lokaci kawo yanzu Usain Bolt bai samu kulob ba al’amarin da ya sa ya yanke shawarar jefar da kwallon mangwaro don ya huta da kuda.

Rahotanni sun ce Bolt bai amince da tayin albashin da kulob din ya yi masa ba, al’amarin da ya sa suka raba gari.

Ganin haka ne ya yanke shawarar daina buga kwallon kafa inda ya ce zai koma harkar kasuwanci, kamar yadda ya sanar da kafar watsa labaran wasanni ta ESPN.

Bolt mai shekara 32 shi ne zakara a bangaren gasar tsere ta duniya inda ya samu nasarar lashe lambobin zinare masu yawa a gasannin Olamfik daban-daban da aka yi a Beijing na kasar Sin da na birnin Landan da kuma a birnin Rio na Brazil da hakan ya sa ya zama dan tseren da ya fi kowane yawan lashe lambobin zinare a tarihin gasar.