Bayan ɓarkewar cutar kwalara a Jihar Legas da wasu jihohi, Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan kare yara daga kamuwa da cutar.
UNICEF ta kuma yi kira da a haɗa kai don hana yaɗuwar cutar, wanda hakan ka iya kawo cikas ga harkar koyarwa a makarantu.
- An samu ƙaruwar rashin tsaro a Najeriya — Rahoto
- UAE ta kusa fara bai wa ’yan Najeriya biza — Keyamo
Shugabar UNICEF a Legas, Celine Lafocrier, wadda ta yi kiran a ranar Litinin, ta ce ɓarkewar cutar kwalara na shafar ƙananan yara masu tasowa.
A cewar Lafoucriere, waɗannan rukunin na yara na fuskantar hatsari game da kiwon lafiyarsu musamman yara da matasa masu zuwa makarantu.
Ta shaida cewar yara na yawan fuskantar cutar bushewar maƙoshi da kuma hatsarin mutuwa fiye da kowa.
“Saboda haka, akwai buƙatar gaggawa na samar da tsarin tsafta, ingantacciyar hanyar samun ruwa mai tsafta, wanke hannu akai-akai da sabulu don yaƙi da cutar a makarantu,” in ji ta.
Sai dai Lafoucrier ta nemi a wayar da kan jama’a kan cutar kwalara da matakan kariya a wani ɓangare na ƙoƙarin magance matsalar.