✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

UNICEF ta gargaɗi gwamnati kan ɓarkewar Kwalara a makarantu

UNICEF ta yi gargaɗi kan yadda cutar na iya kawo cikas ga harkar koyarwa a Najeriya.

Bayan ɓarkewar cutar kwalara a Jihar Legas da wasu jihohi, Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan kare yara daga kamuwa da cutar.

UNICEF ta kuma yi kira da a haɗa kai don hana yaɗuwar cutar, wanda hakan ka iya kawo cikas ga harkar koyarwa a makarantu.

Shugabar UNICEF a Legas, Celine Lafocrier, wadda ta yi kiran a ranar Litinin, ta ce ɓarkewar cutar kwalara na shafar ƙananan yara masu tasowa.

A cewar Lafoucriere, waɗannan rukunin na yara na fuskantar hatsari game da kiwon lafiyarsu musamman yara da matasa masu zuwa makarantu.

Ta shaida cewar yara na yawan fuskantar cutar bushewar maƙoshi da kuma hatsarin mutuwa fiye da kowa.

“Saboda haka, akwai buƙatar gaggawa na samar da tsarin tsafta, ingantacciyar hanyar samun ruwa mai tsafta, wanke hannu akai-akai da sabulu don yaƙi da cutar a makarantu,” in ji ta.

Sai dai Lafoucrier ta nemi a wayar da kan jama’a kan cutar kwalara da matakan kariya a wani ɓangare na ƙoƙarin magance matsalar.