Ƙasashen Rasha da Ukraine sun yi musayar fursunonin yaƙi 230 a tsakaninsu, inda kowace ta karɓi sojoji 115 da ke tsare a hannunsu.
Musayar fursunonin na zuwa ne bayan da sojojin Ukraine ke ci gaba da kutsawa cikin Rasha a wani yanayi da shugaba Volodymyr Zelensky, yayin jawabin da ya gabatar a ranar Asabar.
- Ambaliya: Mutum 6 sun rasu, 2,000 sun rasa muhalli a Adamawa
- An soma biyan ma’aikata sabon albashi mafi ƙaranci a Adamawa
Ya ce Moscow ba ta da masaniyar cewa yaƙin da ta ƙaddamar a maƙwabciyarta zai dawo cikin ƙasarta.
A jawabinsa na ranar ‘yanci da Ukraine ta saki, Zelensky ya sake jinjina wa dakarunsa baya ga sake ba su ƙwarin gwiwar ci gaba da kutsawa sassan Rasha.
Duk da yadda dakarun Ukraine ke ci gaba da kurɗawa Rasha har yanzu ƙasar ba ta mayar da martani ta hanyar kai farmaki ba.
Zelensky, ya sanya hannu kan wata sabuwar doka da ta haramta aiwatar aƙidar kiristanci Orthodox irin na Rasha baya ga rufe dukkanin majami’un da ke bin aƙidar.
Matakin Zelensky na zuwa kwana ɗaya bayan Amurka ta sake bashi tallafin makamai don yaƙar Rasha.