✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uganda ta haye gasar cin Kofin Afirka bayan shekara 38

kasar Uganda ta samu damar hayewa zuwa gasar cin Kofin Nahiyar Afirka da za a yi a badi a&nbsp kasar Gabon bayan shekara 38 ba…

kasar Uganda ta samu damar hayewa zuwa gasar cin Kofin Nahiyar Afirka da za a yi a badi a&nbsp kasar Gabon bayan shekara 38 ba ta samu damar haka ba.
kasar ta haye ne bayan ta doke kasar Comoros da ci daya mai ban haushi a ranar Lahadin da ta gabata a wasan karshe na neman gurbi a gasar da suka yi a babban filin wasa na kasar Uganda da ke Kampala.
Alkalin wasa yana hura tashi daga wasan ne sai daukacin magoya bayan kungiyar suka mamaye filin wasan don nuna murnarsu.
Makada da mawaka a ranar sun baje kolin inda ta kai har sai da gari ya waye al’ummar kasar ba su daina cashewa ba.
Shugaban kasar Uganda Yoweri Musebeni da ya karbi ragamar mulkin kasar tun 1986 shi ma ba a bar shi a baya ba wajen nuna farin cikinsa a kan wannan namijin kokarin da ’yan kwallon kasar suka nuna.&nbsp Jim kadan bayan an tashi daga wasan ne Shugaban ya aike musu da sakon godiya a shafin sadarwarsa na Twitter inda ya yi alkawarin yi musu goma ta arziki a kan wannan bajinta da suka nuna.
Uganda dai ba ta taba hayewa gasar cin Kofin Afirka ko na duniya ba. Wannan nasara da Uganda ta samu ya sa kasar ta hade da kasashen Burkina Faso da Botswana da Tunisiya da Togo da Dimokuradiyyar Kongo da suka haye gasar.
Sauran kasashen sun hada da Aljeriya da Kamaru da Masar da Ghana da Guinea Bissau da Kwaddebuwa da Mali da Maroko da Senegal da Zimbabwe da kuma mai masaukin baki Gabon a gasar da za ta gudana daga ranar 14 ga Janairu zuwa 5 ga Fabrairun 2017 a Gabon.