✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

UEFA ta fito da sabon tsari a Gasar Zakarun Turai

Hukumar kwallon kafa a Nahiyar Turai (UEFA) ta ce daga kakar wasa mai zuwa za a fara amfani da sabon tsari a gasar Zakarun Kulob…

Hukumar kwallon kafa a Nahiyar Turai (UEFA) ta ce daga kakar wasa mai zuwa za a fara amfani da sabon tsari a gasar Zakarun Kulob na Turai.

A sabon tsarin, kamar yadda UEFA ta sanar a ranar Talatar da wuce, an nuna dan kwallo zai iya buga gasar a kulob daban-daban a kakar wasa daya idan ya canja sheka. Ke nan idan dan kwallo ya fara yin gasar a wani kulob sai kuma ya canja sheka a tsakiyar kakar wasa, to an amince zai iya ci gaba da buga gasar. Wannan tsari zai fara aiki ne a kakar wasa mai zuwa ta 2018/2019 kamar yadda Hukumar ta sanar.  Sannan a sabon tsarin za a amince kowane kulob da ke gasar ya rika canjin ’yan kwallo sau hudu maimakon sau uku da ake yi a halin yanzu. 

Hukumar ta ce canja dan kwallo a karo na hudun zai faru ne a matakin zagaye na biyu kuma shi ma sai an kara lokaci bayan an kwashe minti 90 ana fafatawa ba tare da wani kulob ya samu nasara ba. A lokacin da aka yi karin minti 30 (Edtra-time) ne za a amince wa kulob din ya yi canji na hudu.

Sannan hukumar ta ce daga kakar wasa mai zuwa, duk gasannin da take shiryawa  na Zakarun Turai da kofunan Europa League da UEFA Super Cup za a rika yin su ne a tsakanin karfe 5:55 na yamma zuwa karfe 8:00 na dare agogon Najeriya, ba kamar yadda ake yi a yanzu a tsakanin karfe 7:45 na dare zuwa karfe 8:45 na dare agogon Najeriya ba.

Sannan idan wasannin suka kai matakin zagaye na biyu har zuwa karshe, za a yi su ne da karfe takwas na dare agogon Najeriya har zuwa wasan karshe.

Duk wadannan canje-canje za su fara aiki ne daga kakar wasa mai zuwa ta 2018/2019, kamar yadda hukumar ta sanar.