Janar Ibrahim Badamasi Babangida na ɗaya daga cikin shugabannin Najeriya masu ƙarfin faɗa aji har bayan saukarsu daga mulki.
Ya kawo sauye-sauye a tsarin tafiyar da gwamnati da ma harkokin siyasa baki ɗaya.
Kodayake ya samar da muhimman abubuwan cigaban ƙasa amma an fi tuna mulkinsa da shirin SAP na matse bakin aljihun gwamnati.
Tuna Baya: Tarihin Janar Muhammadu Buhari
Tuna Baya: Tarihin Shugaban kasar Najeriya Alhaji Shehu Shagari
Ya kuma yi ƙaurin suna wurin tufka da warwar a da har ta kai ana yi masa laƙabi da Maradona, sunan wani ɗan ƙwallon Argentina da ya shahara kan yanka a filin wasa.
Bayan da ya sauka daga mulki ya yi yunƙurin komawa a matsayin farar hula amma bai samu nasara ba.
Sai dai kusan duk gwamnatin da aka kafa bayan saukarsa da sa hannunsa ko sahhalewarsa a ciki.