✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tukwici ga mai azumi

Daren Lailatul Kadari ya fi wata dubu wajen alheri.

A yayin da muka shiga watan azumin Ramadan din bana, insha Allahu daga yau za mu fara gabatar da wannan rubutu daga littafin Ramadaniyyat, wanda Dokta Ahmad Adam Kutubi (SP) na Rundunar ’Yan sandan Najeriya, ya turo mana.

Muna fata za a amfana da darussan da ke cikinsa:

Ma’anar azumi:

Abin da ake nufi da azumi shi ne “Kamewa da barin ci da sha da saduwa da iyali da duk wani abu da zai shiga ciki, daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana.”

Yin wannan ibada daya ce daga cikin rukunan Musulunci guda biyar.

Don haka ne wajibi ne a kan Musulmi da Musulma baligai masu hankali da lafiya da za su iya yin azumi su yi shi.

Kuma hanyoyi uku ne ake bi don ganin wata:

1. In an samu mutum biyu adalai sun ga wata,sai a tashi da azumi.

2. Idan mutane da yawa suka ga wata kamar a ce gari kaza an ga wata, to, sai a tashi da azumi.

3. Cikar watan Sha’aban kwana talatin cif, to ranar da za ta biyo baya Ramadan ne, domin a Musulunci ba wata mai kwana talatin da daya.

Annabi (SAW) ya ce; “Wata ashirin da tara ne, to, idan gari ya yi duhu sai ku cika Sha’aban talatin daidai.

A wani Hadisin kuma Annabi (SAW) yana cewa: “Ku yi azumi idan aka ga wata kuma ku sha idan aka gan shi, amma idan wata ya buya muku, to sai ku cika kidayar watan Sha’aban talatin.”

Wato wannan Hadisi ya nuna idan Sha’aban ya cika talatin daidai sai a tashi da azumi washegari ko an ga wata ko ba a gani ba.

Ayoyin da suka yi magana a kan azumi: Allah Ya ce a cikin Alkur’ani Mai girma: “Ya ku wadanda suka yi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan mutanen da suke gabaninku, tsammaninku za ku ji tsoron Allah (takawa). Kwanuka ne kidayayu.

To, wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuma yana a kan tafiya, sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na daban.

Kuma a kan wadanda suke yin sa da wahala akwai fansa, ciyar da matalauci, sai dai wanda ya kara alheri, to shi ne mafi alheri a gare shi.

Kuma ku yi azumi (da wahalar) ne mafi alheri a gare ku, idan kun kasance kuna sani.

Watan Ramadan wanda aka saukar da Alkur’ani a cikinsa, shiriya ne ga mutane da hujjoji bayyanannu da shiriya da rarrabewa.

To, wanda ya halarta daga gare ku a watan, sai ya azumce shi, kuma wanda ya kasance majinyaci ko kuwa a kan tafiya, sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na daban.

Allah Yana nufin sauki a gare ku, kuma ba Ya nufin tsanani a gare ku, kuma domin ku cika adadin, kuma domin ku girmama Allah a kan Ya shiryar da ku, kuma tsammaninku, za ku gode.

Kuma idan bayinNa suka tambaye ka daga gare Ni, to lallai ne Ni makusanci ne.

Ina karba kiran mai kira idan ya kira Ni. Saboda haka su nemi karbawaTa, kuma su yi imani da Ni, tsammaninsu, su shiru.

An halatta a gare ku a daren azumi, yin jima’i zuwa ga matanku, su tufa ne a gare ku, kuma ku tufa ne a gare su.

Allah Ya sani, lallai ne ku, kun kasance kuna yaudarar kanku. Saboda haka Ya karbi tubarku, kuma Ya yafe muku.

To, yanzu ku rungume su, kuma ku nemi abin da Allah Ya rubuta muku. Kuma ku ci kuma ku sha har silili fari ya bayyana a gare ku daga silili baki daga alfijir, sa’an nan kuma ku cika azumi zuwa ga dare.

Kuma kada ku rungume su alhali kuma masu I’itikafi a cikin masallatai.

Wadancan iyakokin Allah ne. Don haka kada ku kusance su, kamar haka ne Allah Yake bayyana ayoyinSa ga mutane, tsammaninsu, za su yi takawa.” (Q:2: 183 – 188)

Hikimar wajabta azumin Ramadan:

Ramadan suna ne na watan tara daga cikin watannin Musulunci, shi ne kuma watan da Allah Ya ambace shi karara.

Hikimar da tasa aka wajabta mana azumi a cikinsa ita ce don a tsarkake rai ne da kuma sanya mata tsoron Allah don ta cancanci dacewa gobe Lahira.

Ladubba wajibabbu ga mai azumi:

1. Wajibi ne ga mai azumi ya tashi da niyyar cewa azumi ibada ce cikin maganganunsa da ayyukansa.

2. Ya nisanci abubuwan da aka haramta a cikin maganganunsa da ayyukansa kuma ya tsare ganinsa da jinsa da tafiyarsa daga haramtattun abubuwa.

Wadannan wajibi ne ga mai azumi ya kiyaye su in yana so azuminsa ya karbu a wajen Allah.

Abubuwan da ake so ga mai azumi:

1. Jinkirta yin sahur.

2. Gaggauta yin bude-baki.

3. Yawaita karatun Alkur’ani Mai girma.

4. Yawaita addu’o’in alheri.

5. Yawaita sadaka.

6. Yawan ambaton Allah da tsarkake Shi da sauran ayyukan alheri.

Falalar watan Ramadan

1. A cikinsa aka saukar da AIkur’ani: Allah Ya ce: “Watan Ramadan ne wanda aka saukar da Alkur’ani a cikinsa.”

2. Ana gafarta zunubai a cikinsa: Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya yi azumin watan Ramadan yana mai imani yana mai kyautatawa, to an gafarta masa abin da ya gabata na laifuffukansa.” Buhari ya ruwaito.

3. Ana amsar addu’ar mai Azumi: Annabi (SAW) ya ce: “Ana karbar addu’ar mutum uku: mai azumi lokacin bude-baki da shugaba mai adalci da wanda aka zalunta.”

4. Daren Lailatul Kadari: Allah Ya ce “Daren Lailatul Kadari ya fi wata dubu wajen alheri.

5. Ana daure shaidanu: Domin Annabi (SAW) ya ce: “Idan Ramadan ya zo ana daure shaidanu kuma a bude kofofin Aljanna.”

6. Yin Umara a Ramadan yana daidai da aikin Hajji.

Abubuwan da suka halatta ga mai azumi:

1. Yin asuwaki da rana da itacen da ba shi da dandano, wato dadi ko zaki ko bauri ko wani dandano daban.

2. Yin tafiya cikin watan azumi in bukatar haka ta taso.

3. Zuba ruwan sanyi a kai ko wanka da ruwan sanyi in zafi ya yi yawa don a ji sanyi-sanyi.

4. Cin abinci da daddare amma ban da rana.

5. Shan abin sha na halal da daddare.

6. Saduwa da iyali da daddare amma ba da rana.

7. Amfani da magani na shafawa amma in na sha ne sai da daddare.

8. Yin allura da rana, ba laifi, idan ba ta da dandano a baki, amma ta karin ruwa ba ta halatta da rana a azumi ba. Dalili kuwa idan ciwon zai kai a kara wa mutum ruwa, to, ya halatta ya sha azumin in ya samu sauki sai ya rama abin da ya sha.

9. Shafa turare idan ba na hayaki ba ne.

10. Sanya tozali da daddare ban da rana.

Abubuwan da ke karya azumi

1.Saduwa da iyali da rana.

2. Fitar da maniyyi da rana na karya azumi sai dai in mafarki aka yi ya fita, to, wannan azumi bai karye ba.

3. Cin abinci da rana.

4. Shan abin sha da rana.

5. Wanda ya kago amai da gangan azuminsa ya karye.

6. Fitar jinin haila ga mace mai azumi.

7. Fitar jinin biki na karya azumi.

Dokta Ahmad Adam Kutubi (SP) Hedikwatar ’Yan sanda ta Zone 7, Wuse Zone 3, FCT, Abuja 08036095723, 07045472372