A yau kuma ga ci gaba da wannan rubutu daga littafin Ramadaniyyat, wanda muka sanya masa suna ‘Tukuicin Girma ga mai azumi’ wanda Ustaz Ahmad Adam Kutubi (SP) na Rundunar ’Yan sandan Najeriya, ya fassara. Da fatan za a amfana da darussan da ke cikinsa.
Muna amfani da wannan dama wajen rokon Allah Ya tausaya mana Yayaye mana wannan jarrabawa ta cutar Kurona da take barazana ga Bani Adam. Ya Allah! Saboda albarkar da Ka sanya a watan Ramadan Ka gagauta kawo mana qarshen wannan annoba ko bala’i da sauran bala’o’in da suke addabarmu ba domin halinmu ba:
Daga Imam SP Ahmad Adam Kutubi
3. Hauka: Babu azumi a kan mahaukaci har sai ya warke.
4. Tsoho tukuf, wanda ba ya iya bambance waxanda ke zuwa wurinsa, to su irin waxannan tsofoffi, maza ne ko mata sai su ciyar da Mudun Nabiyyi guda a mazaunin azuminsu a duk rana har a gama azumin.
5. Haka ma hukuncin yake ga wanda ba zai iya azumi ba, koda lokacin sanyi ne, ko lokacin ruwa, saboda ciwon yunwa ko ciwon qishin ruwa kuma ba a tsammanin zai warke, shi ma zai ciyar da Mudun Nabiyyi kowace rana da ya sha azumin.
Wadanda azumi ya wajaba a kansu:
1. Mai hankali:Azumi wajibi ne a kansa.
2. Musulunci: Domin azumi bai wajaba a kan wanda ba Musulmi ba.
3. Balaga: Domin azumi bai wajaba a kan yaro ba har sai ya balaga; kuma ana gane balagar yaro ta hanyoyi uku:
I. Fitar maniyyi ta hanyar mafarki ko wata hanya daban.
II. Tsirar gashin hammata ko na gaba.
III. Cika shekara 12 ko 15 ga mata ko 15 zuwa 18 ga maza. Ga mata da karin ganin jinin haila.
3. Da tsarkakuwa daga jinin haila ko jinin biqi ga mata.
4. Lafiya: Mara lafiya azumi bai wajaba a kansa ba har sai ya warke.
Wadanda azumi bai wajaba a kansu ba, amma dole su biya:
1. Matafiyi idan ya sha azumi a cikin tafiya dole ne ya biya.
2. Mara lafiya yana iya shan azumi duk lokacin da ya warke sai ya biya abin da ya sha.
3. Mai haila ba azumi a kanta, amma in ta yi tsarki za ta biya abin da ta sha, kuma idan mai haila ta xauki azumi sai jini ya zo mata kafin rana ta fadi, to, azuminta ya vaci, haka kuma idan haila ta dauke mata da rana a Ramadan ba azumi a kanta a sauran wannan wunin sai dai za ta rama azumin ranar da sauran kwanakin da ta sha.
Bugu da kari idan jinin ya dauke kafin fitowar alfijir ko da mintuna kadan ne kafin fitowar alfijir, to, azumi ya wajaba a kanta.
Karin bayani: Shi ma jinin haihuwa (biqi) kamar jinin haila ne cikin dukkan hukunce-hukuncensa.
4. Mace mai shayarwa idan ta ji tsoron danta ba zai samu nonon da za ta shayar da shi ba, sai ta ci abinci, to, tana iya cin abincin bayan azumi ya wuce sai ta ramagwargwadon abin da ta sha. Haka hukuncin yake ga mace mai ciki idan ta ji tsoron abin da ke cikinta, ita ma tana iya shan azumi kuma wajibi ne a kanta ta biya gwargwadon azumin da ta sha bayan ta haife cikin nata.
5. Wanda wani dalili ya sa ya sha azumi kamar ya yi kokari don kuvutar da wata rai
da za ta hallaka saboda gobara ko nutsewa a ruwa, sai wurin kokarin kubutar da wadannan mutane ya sha azumi, to bayan azumin zai rama gwargwadon abin da ya sha.
Sahur da ladarsa:
Sahur shi ne cin abinci a karshen dare kafin fitowar alfijiri da niyyar ibada.
Sahur Sunnah ne don Annabi (SAW) ya ce: “Bambancin azuminmu da azumin Ma’abuta Littafi, shi ne cin abincin Sahur.”
Muslim ya ruwaito. Annabi (SAW) ya ce: “Ku yi Sahur hakika akwai albarka a cikin yin Sahur.” Muslim ya ruwaito.
An samu Hadisi daga Sabit (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Mun yi Sahur da Annabi (SAW) sai ya tashi zai yi Sallah sai na tambaye shi, na ce ayoyi nawa mutum zai iya karantawa a tsakanin kiran Sallah da barin Sahur? Sai Annabi (SAW) ya ce: “Tsakanin kiran Sallah da barin Sahur mutum zai iya karanta ayoyi hamsin.” Buhari ya ruwaito.
Buxa-Baki:
Abin da ake nufi da buda-baki shi ne mai azumi ya ci wani abu ko ya sha wani abu yayin da ya tabbatar da rana ta faxi, yin haka yana daga cikin abin da ake so, domin Annabi (SAW) ya ce: “Al’ummata ba za su gushe (cikin nasara) ba, matukar suna gaggauta buda-baki.” Buhari ya ruwaito Hadisin.
Abin da ake Buxa-Baki da shi:
1, Kayan marmari, kamar lemu ko ayaba ko gwaiba da sauran kayan marmari.
2. Dabino kowane iri danye ko busasshe.
3. In kuma ba a samu kayan marmari ko dabino ba, sai a yi buxa-baki da ruwa.
Saboda Annabi (SAW) ya kasance yana buda-baki ne kafin ya yi Sallah, kuma yana yi ne da korayen abubuwa wato ’ya’yan itatuwa ke nan, kamar lemu da sauransu, in kuma bai samu ’ya’yan itatuwa ba, sai ya yi da dabino, in babu sai ya yi da ruwa.
(Tirmizi ya ruwaito).
Addu’ar Buda-Baki
“Allahumma lakas sumtu wa ala rizikika afdartu, Allahumma taqabbal minni”
Ma’ana: “Ya Allah gare Ka na yi azumi kuma da arzikinKa na yi buda-baki, Ya Ubangiji Ka karvi wannan azumi da na yi.” Wadanda ake karvar addu’o’insu:
Daga cikin wadanda ake karvar addu’o’insu akwai addu’ar mai azumi yayin buxa-baki. Domin Annabi (SAW) ya ce: “Mutum uku ana karbar addu’o’insu:
Shugaba mai adalci da wanda aka zalunta da mai azumi lokacin buda-baki.
Ladan wanda ya ciyar da mai azumi:
Bai wa mai azumi abin buxa-baki yana daga cikin sadaka mai lada da yawa, domin Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya ciyar da mai azumi yayin buda-baki, to za a ba shi lada kamar ladar mai azumin ba kuma tare da an rage wa mai azumin ladarsa ba.”
Tirmizi ne ya ruwaito.
Hadisai masu rauni ko na karya a kan azumi:
1. Daga cikin hadisan da ake dangantawa ga Annabi (SAW) waxanda wadansu malamai suke gani da’ifai ne akwai:
i. “Ku yi azumi za ku samu lafiya.” ii. “Azumin watan Ramadan yana rataye a tsakanin sama da kasa har sai mutum ya ba da Zakkatul Fitri.”
Wadansu malamai suna ganin cewa irin wadannan hadisai, suna daga cikin hadisan kwadaitarwa da kuma tsoratarwa don kada a yi sake.
Sallar Tarawihi:
Sallar Tarawihi tana daga cikin sallolin nafila da ake yi a cikin azumi kuma abin da ya sa ake kiranta da Tarawihi, shi ne saboda zaman da ake yi a kowace raka’a biyu a yi sallama, wato an xauki wannan kamar zaman hutu ne. Yin Sallar Tarawihi Sunnah ce. Gwargwadon raka’o’inta kuma goma sha uku (13) ne duk da Shafa’i daWutiri.
A wata ruwayar kuma an ce goma sha xaya ne (11) duk da Shafa’i da Wutiri, saboda Hadisin da A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ruwaito, cewa: “Annabi (SAW) ba ya qari a kan raka’o’i goma sha xaya da yake yi a Ramadan ne ko ba a Ramadan ba.”
Nafilfilin dararen goma na qarshe na watan Ramadan:
Daga A’isha (Allah Ya yarda da ita),ta ce: “Annabi (SAW), ya kasance idan goman qarshe na watan Ramadan ya zo, to ba ya barci, sai ya ta da mutanen gidansa maza da mata ya duqufa ga nafilfili har qarshen watan Ramadan.” Buhari ya ruwaito.
Imam SP Ahmad Adam Kutubi 08036095723