Tuffa na daya daga cikin kayan marmari da ake amfani da su don kara lafiya da nishadi, kuma kamar yadda aka sani ko aka saba yana zuwa ne a launukan ja da rawaya da kore kuma a farashi matsakaici da kusan kowa zai iya saye.
Sai dai abin da mutane ba su sani ba shi ne akwai tuffa mai launi baki da farashin daya ya kai kimanin Naira dubu biyar.
- Sababbin finafinan Kannywood da za a fara a bana
- Mun soke lasisin duk makarantu masu zaman kansu — Gwamnatin Yobe
Wannan tuffa shi ake yi wa lakabi da ‘Bakin lu’u-lu’u mai daraja’, kuma farashinsa ya zama gagara saye sai an shirya domin ana sayar da kowane daya a kan Rupee 500, (Kimanin Naira dubu 5 da 394).
Wannan tuffa mai matukar daraja ana samunsa ne kadai a yankin Nyingchi da ke tsaunukan Tibet a kasar China.
Shuka da lokacin girbinsa ya bambanta da na sauran ’ya’yan itatuwa irinsa.
A yanayin Tibet mai manyan tsaunuka a kuma can samansu ake rainon dan itacen, inda ake kula da yadda hasken rana ke taba shi tare da daidaita yanayin sanyi da zafi da kuma dumamar yanayi duk a wajen raino da hakan kan taimaka wajen ba shi wannan launi na daban.
Haka kuma, ba kamar sauran itatuwan tuffa ba da suke yin shekara biyu ko uku kafin su girma har a ci amfaninsu.
Itaciyar bakin tuffa sai an jure, domin shekara takwas take yi kafin ta girma ga kuma yanayin tsauni da ake shuka ta, ga tsawo da kuma sauran wahalhalu na jigila.