✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon Sakataren Tsaron Amurka Donald Rumsfeld ya mutu

Marigayi Rumsfeld na daya daga cikin manyan da suka haddasa yakin Iraki.

Tsohon Sakataren Tsaron Amurka, Donald Rumsfeld, ya mutu yana da shekara 88 kamar yadda iyalansa suka sanar a ranar Laraba.

Marigayi Rumsfeld na daya daga cikin manyan da suka haddasa yakin Iraki.

Ya yi aiki zamanin shugaba George W Bush, inda ya kasance babban mai jagorantar yaki da ta’addanci na gwamnatin Amurka a lokacin.

Dakarun Amurka sun kaddamar da yaki a Afghanistan bayan harin 9/11, inda a shekarar 2003 Amurka ta mamaye Iraki.

Shi ne wanda ya jagoranci harin da sojojin Amurka suka kai wa ’yan Taliban masu goyon bayan Usama Bn Laden da sauran shugabannin kungiyar Al Qaeda.

Shekaru biyu bayan haka kuma ya jagoranci mamayar da Amurka ta kai wa Iraki da zummar kawai da shugabanta na wancan lokaci, Sadam Hussein.

Mista Rumsfeld ya yi murabus a 2006 sakamakon abin da ya biyo bayan yakin Iraki, amma ya kare kansa.