Tsohon Ministan Ilimi kuma tsohon dan takarar Shugabancin Kasar nan a karkashin tsohuwar jam’iyyar ANPP, Dauda Birma ya rasu yana da shekara 81 a duniya.
Abubakar Dauda Birma, babban dansa wanda shi ne Manajan-Darakta a Kamfanin dillancin man fetur mai suna South Chad Limited, shi ne ya tabbatar wa da Aminiya rahoton rasuwar mahaifin nasu.
- Kwamishina ya yi murabus saboda rashawa ta yi kaka gida a gwamnatinsu
- Rikicin yankin Gulf: Saudiyya ta Qatar sun sasanta
- Sergio Ramos da Messi za su koma PSG, Chelsea za ta raba gari da Lampard
Birma wanda shi ne yake rike da sarautar gargajiya ta Sarkin Gabas a Adamawa ya rasu ne ranar Talata a Asibiti Kwararru na Yola bayan ya yi fama da gajeruyar rashin lafiya.
Marigayi Birma ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya 12 da kuma jikoki 28.
Kafin rasuwarsa, ya kasance mamba a Majalisar Amintattu ta Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabas.
Ya yi wa Najeriya hidima a matakai daban-daban ciki har da kasancewarsa mamba a Kwamitin Sasanci na Kasa.
Marigayin wanda ya nemi takarar shugabancin kasar nan har sau biyu, shi ne dan takarar da ya jagoranci wasu masu neman takarar kujerar Shugaban Kasa da suka janye wa Shugaba Muhammadu Buhari a babban zabe na 2003.