✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Minista ya zama Sakataren Gwamnatin Jihar Borno

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya naɗa tsohon Minista a ma’aikatar noma da raya karkara, Malam Bukar Tijjani a matsayin Sakataren Gwamnati. Kakakin gwamnan,…

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya naɗa tsohon Minista a ma’aikatar noma da raya karkara, Malam Bukar Tijjani a matsayin Sakataren Gwamnati.

Kakakin gwamnan, Malam Isa Gusau ne ya sanar da wannan naɗin ranar Laraba.

Sanarwar ta ce Gwamnan Zulum ya yi la’akari ne da ƙwarewar da Bukar Tijjani ya nuna lokacin da ya yi minista daga Yuli 2011 zuwa Satumba 2013 da kuma muƙamin da ya riƙe na Mataimakin Darakta Janar na Hukumar Abinci da Harkokin Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO).

Zulum ya hana gwangwan a Borno

Kwamandojin ’yan ta’adda 2 sun mika wuya ga sojoji a Borno

Malam Bukar Tijjani ya kuma riƙe shugabancin shirin samar da abinci na ƙasa da kuma shirin bunƙasa noman rani na Bankin Duniya a Najeriya wanda aka fi sani da Fadama.

Tsohon ministan mai shekaru 62 ɗan asalin ƙaramar hukumar Dikwa ne amma haifaffen garin Damasak dake Arewacin jihar Borno.

Ya yi digirin farko a Amurka a 1984 sannan ya yi digirinsa na biyu a Ingila a 1989 duk a fannin noma.

Sanarwar ta ce, a matsayin Gwamna Zulum na farfesa a fannin noman rani ya naɗa tsohon ministan ne a matsayin Sakataren Gwamnati domin taimakawa wurin bunƙasa noma da wadatar da jihar Borno da abinci.