Tsohon mai tsaron gidan kulb din Flying Eagles, Wilfred Agbnabbare ya rasu a ranar Talatar da ta gabata bayan ya yi fama da cutar kansa a asibitin kwararru na kasar Sifen.
Rahotanni sun nuna cewa Wilfred wanda ya rasu yana dan kimanin shekaru 48 da haihuwa ya fara kwanciya ne a wani asibiti da ke kasar Amurka amma saboda tsadar kudin asibitin aka mayar da shi Sifen a makon da ya gabata.
Kulab dinsa mai suna Rayo ballecano da ke kasar Sifen ya yunkuro don amsa kiran da marigayin ya yi masa na taimaka masa da biyan kudin asibiti inda suka biya euro dubu 21 kwatankwacin Naira miliyan 4 da dubu 800 don a yi masa magani.
Aminiya ta gano cewa kulab dinsa yana kan taimakawa ’ya’yansa uku don su samu takardar izinin shiga Sifen su gana da mahaifinsu amma kafin su kai ga samun takardar mutuwa ta yi halinta.
Wilfred wanda ya taba zama tsohon mai tsaron gidan kulob din New Nigeria Bank ya yi ritaya a harkar kwallon kafa yana da shekara 31 a duniya.
Abokanensa da suka yi wasa tare a kulob din Flying Eagles sun bayyana shi a matsayin dan wasa mai ladabi da biyayya.
Rahotannin sun nuna cewa marigayin ya zama dan wasa kulab din Flying Eagles na hudu da ya rasu. Ya mutu ya bar mata daya da ’ya’ya uku tare da mahaifiyarsa da mahaifinsa.