✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon kocin ABS zai kai karar Bukola Saraki

Tsohon kocin kulob din Abubakar Bukoka Saraki (ABS FC) da ke Ilorin Yusuf Salihu ya yanke shawarar kai karar kulob din ne saboda rashin biyansa…

Tsohon kocin kulob din Abubakar Bukoka Saraki (ABS FC) da ke Ilorin Yusuf Salihu ya yanke shawarar kai karar kulob din ne saboda rashin biyansa albashi har na tsawon watanni 23.
Salihu Yusuf ne ya horar da kulob din a bara inda kulob din ya kasance na biyu a jerin kungiyoyin da suka fafata a gasar rukunin ’yan dagaji (amateur league).  Sai dai duk da wannan kokari da ya yi kulob din ya ki biyansa albashi da alawus-alawus na tsawon watanni 23 ba tare da wani dalili ba.
Tsohon kocin ya ce duk kokarin da ya yi na ganin kulob din ya biya shi basussukan da yake bi bashi abin ya ci tura.  Ya ce abin mamakin ma shi ne yadda kulob ya dauki sabon mai horarwa inda yake biyansa albashin Naira miliyan daya da rabi a duk wata amma kuma ya kasa biyansa basussukan da yake bi bashi.
“Na yi hakuri, na bi duk hanyoyin da suka kamata na bi don ganin an biya ni hakkokina amma abin ya ci tura.  Yanzu haka an koro yarana daga makaranta baya ga dimbin matsalolin da suka dabaibaye ni don haka na yanke shawarar shigar da kara kotu.  Amma kafin nan ina kira ga mai kulob din Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Bukola Saraki da ya yi wa Allah ya sanya baki a biyani, in ba haka ba zan shigar da kara”, inji Salihu.