✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon Fira Ministan Mali Boubèye Maïga ya rasu

Ya shafe tsawon wata uku yana jinya a wani asibiti a Bamako.

Tsohon Fira Ministan kasar Mali, Soumeylou Boubèye Maïga da hukumomin kasar suka tsare, ya rasu a ranar Litinin a wani asibiti da ke Bamako, yana da shekara 67 a duniya.

Iyalan tsohon Fira Ministan ne suka sanar da rasuwarsa ga manema labarai.

Tun a cikin watan Agusta aka tsare Soumeylou Boubeye Maiga, wanda ya yi Fira Minitsa daga watan Dismambar 2017 zuwa Afrilun 2019, bisa zargin almundahana, a wani bangare na bincike kan yaki da cin hanci da gwamnati sojar kasar ke yi.

Binciken na da alaka da wata kwangilar sayen kayayyakin aikin soja.

Wata uku da suka gabata aka kwantar da Mista Soumeylou Boubèye Maïga a wani asibiti a Bamako sakamakon rashin lafiya da yake fama da ita.

Tun da farko likitoci sun bukaci fitar da shi kasar waje don nema mishi lafiya, amma hukumomin rikon kwaryar sojin suka yi watsi da bukatar hakan.