✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon dan kwallon Bendel Insurance ya rasu

A ranar Litinin da ta wuce ne aka samu labarin rasuwar tsohon dan kwallon kulob din Bendel Insurance George Omokaro. Ya rasu ne a gidansa da…

A ranar Litinin da ta wuce ne aka samu labarin rasuwar tsohon dan kwallon kulob din Bendel Insurance George Omokaro.

Ya rasu ne a gidansa da ke Edo bayan ya yi fama da doguwar jinya.

Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa (NFF) ta bakin Sakatare-Janar Dokta Muhammad Sanusi ta tabbatar da rasuwar tsohon dan kwallon.

NFF ta ce ta kadu matuka da ta samu labarin rasuwar dan kwallon da ya ba da gudunmawa wajen ci gaban kwallon kafa a kasar nan.

“Muna yi wa iyalan George Omokaro ta’aziyya game da wannan rashi da muka yi.  Muna addu’ar Allah Ya ba iyalansa  hakurin juriyar rashinsa,” inji sanarwar da Doka Sanusi ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai.

Tun a shekarar 2016 George Omokaro ya kamu da rashin lafiya bayan wata ’yarsa ta rasu.  Tun daga wancan lokaci har ya rasu a ranar Litinin da ta wuce yake kwance yana jinya saboda jimamin rashinta.