✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsarkakan kalaman dushewar hangen nesa

Da a ce shugabannin Najeriya za su cika alkawuran da suka dauka, su yi aikin da ya dace da kalamansu, da kasar nan ta kyautatu…

Da a ce shugabannin Najeriya za su cika alkawuran da suka dauka, su yi aikin da ya dace da kalamansu, da kasar nan ta kyautatu fiye da yadda take a halin yanzu. Abin takaicin dai shi ne, suin kasa katabus. Domin a Alhamis din makon jiya ne, shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi karaji wajen nuna farin cikinsa, wacce irin kasaitacciyar kasa Najeriya za ta kasance, idan ta samu shugabancin da ya bunkasa tattalin arzikinta, ya kuma yi tasiri a kan al’umma.
Da yake jawabi a idan gwmanati, wajen bikin kaddamar da Hukumar Kula da kanana da matsakaitan Masana’antu (MSME), shugaban kasa ya yi ta kwakwazo kan albarkatun Najeriya, da kuma abubuwan da take da su wadanda suka sanya ta cancanci zama kasaitacciya. Saboda haka ya yanke cewa ya rage ruwan shugabanni su yi aiki don tabbatar komai na gudana.
Wadannan “abubuwa” na nufin warware daukacin “matsalolin tattalin arziki kan al’amuran da suka shafi jawo kowa da kowa tare da samar da dukiya,” a cewarsa. ‘Wannan kasar tamu nan ne matasanmu ke da aikin yi, kuma makomar arzikin mutanenmu na hannunsu. Dole ta kasance kasar da aka fatattaki talauci, ta yadda al’ummarmu za ta zauna cikin mutunci. Wannan ita ce Najeriya da dole mu yi aiki wajen tabbatar da ita.’
Hangen Jonathan ya dusashe game da abin da ’yan Najeriya ke gani a yau. Matsalar tsaro daya ce kawai daga cikin abubuwan da suka kaimu ga halin da muke ciki; amma ba ita ce jigo ba. kasashe na bunkasa a lokutan da ake fama da ire-iren wadannan kalubalen. Jigon lamari dai, shi ne, tsarin tafiyar da shugabanci ya fitar da managartan tsare-tsare, kuma a kasance cikin shiri wajen ganin an aiwatar da su.
Akwai kananan da amtsakaitan masana’antu fiye da dubu 40 da ke jihohin fadin tarayyar kasar nan. Babban Bankin Najeriya na da Asusun Raya kananan da Matsaiktan Masana’antu (MSMDF), wanda aka kaddamar a watan agustar 2013, da kudin fara hada-hada Naira biliyan 220. An ware kaso na musamman ga bankunan kasuwanci daga wannan asusu da ke karkarshin Babban Bankin Najeriya (CBN), inda za su rika bayar da rance ga daidaikun mutane da kuma masana’antu  karkashin tsarin.
A bayyane yake karara, wannan kasar ba ta rasa tsare-tsaren bunkasa kananan da matsakaitan masana’antu ba, sai dai a gaskiya, akwai yiwuwar wani ya hango cewa kirkiro wata hukuma a karkashin kulawar mataimakin shugaban kasar Najeriya kara cukurkuda ayyukan hukuma ne, wadanda suke kawo tarnakin bunkasar wannan muhimmin sashe a harkokin tattalin arziki.
Sannan akwai bukatar a jefa ayar tambaya a kan matsalar makamashin lantarki.
Kusan kowa da kowa, har ma da jami’an gwamnati, duk an yarda cewa sashen kula da makamashin wutar lantarki, wani muhimin al’amari ne da daukacin ayyukan raya kasa suka dogara kacokam a kansa. MAtukar ba a warware matsalar wannan sashe ba, to bunkasar tattalina rzikin da Shugaban kasa ke hankoron gani a Najeriya zai matukar girgiza. Wani muhimmin sashen shi ne fannin aikin gona. An fahimci tsare-tsaren gwamnati game da wannan sashe, bisa la’akari da kason da aka ware masa a kasafin kudi. A shekarar 2013, kasafin kudi na tarayya ya ware wa fannin noma kason Naira biliyan 83, al’amarin day a yi kasa kasha 1.7 cikin 100 na daukacin kudin da aka kimanta kashewa a kasafin, sannan ya yi kasa da kasha 10 cikin 100 na yawan kudin da kasashen da ke cikin Tarayyar Afirka (AU) suka amince a rika kashe wa sashen a kowace shekara. A wannan shekarar ma, ala’amarin ya kara zama abin takaici, inda aka ware Naira biliyan 66.64 kacal. Ganin cewa Gwmanatin Tarayya ta rage kason da take bai wa fannin noma, sai aka yi has ashen ko kamfanoni masu zaman kansu sun samu damar aiwatar da shirin Gwamnatin Tarayya na bunkasa aikin gona (ATA), don cike gibin da aka samu a shekarar 2014, wajen aiwatar da aiki a aikace. Sabanin hakan ma, sai aka jefa siyasa cikin al’amarin, inda Gwamnati ta amince da (ko ma ta dauki nauyin) Jakadun Gyaran Najeriya (TAN), wadanda aka dora su a kan turbar kambama kai, don cimma burin Jonathan na komawa kan karagar mulki, ya gaji kansa a zaben shekarar 2015, wanda ke karatowa.
Jami’an Gwmanatin Jonathan suna ta gudu ne a kan bagire guda, sannan kowane tsari na wamnati an dora shi a kan wannan manufa. Wannan shi ne dalilin hasashensa na cewa Najeriya na da yawan al’umma mutum miliyan 170, ita ce kasa ta tara a duniya bisa ma’aunin yawan ma’aikata, don haka za ta yi amfani da wannan kadara tata wajen ‘kawo sauyi da ci gaba’, wannan al’amari za a iya tabatar da gaskiyarsa ne kawai idan an nuna adalcin rabo, maimakon kason albarkatu kawai, sannan a aiwatar da su a aikace.