✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsarin IPPIS ya fusata ASUU kan shirin shiga yajin aiki

Kungiyar Malaman Jami’oi ASUU reshen Jami’ar gwamnatin Tarayya ta Kashere da ke jihar Gombe sun yi barazanar tsunduma yajin aiki muddin gwamnatin tarayya taki biyan…

Kungiyar Malaman Jami’oi ASUU reshen Jami’ar gwamnatin Tarayya ta Kashere da ke jihar Gombe sun yi barazanar tsunduma yajin aiki muddin gwamnatin tarayya taki biyan su albashin watan Janairu 2020, inda ake tilasta musu sai sun shiga sabon tsari na bai-daya na biyan albashi dauke da bayanan ma’aikaci ta na’ura (IPPIS).

A taron manema labarai da suka kira a Jami’ar tarayya ta Kashere Shugaban kungiyar ta ASUU reshen Jami’ar Dakta Ahmed Abubakar Yauta, ya bayyana cewa su ba za su shiga wannan tsari na IPPIS ba sai dai a yi amfani da tsarin nan na UTAS wato ‘Universities Transparency and Accountability Solution’.

Dakta Ahmed Yauta, ya ce gwamnatin tarayya na kokarin ganin ta musguna masu ne ko kokarin yi musu bita da kulli kan wannan shiri inda ya kirayi mambobin su da kar su bari wani batanci ya gurgunta musu kungiya.

Kungiyar ta ASUU tayi Allah wadai da yadda Babban Akantan Najeriya ya yi wa wannan al’amari rikon sakainar kashi wanda a cewarsu hakan zai gurgunta harkar ilimi ya mayar da shi baya a Najeriya.

Har ila yau Kungiyar ta ce, rashin adalci ne gwamnati taki biyan wanda ya yi aiki albashinsa inda suka soki hakan da cewa ya sabawa doka, dan haka ya ce su Malaman Jami’a ba su da niyyar shiga wannan tsari na biyan albashi ta IPPIS. Kungiyar tana mai sanar da al’umma da kuma gwamnatin tarayya cewa, sun yanke matsayar cewa muddin suka bibiye su akwai wani reshen jami’a da ba’a biyan albashi ba na watan Janairu suna nan kan bakar su ta ba albashi ba aiki wato ‘No Pay No Work’ ma’ana za su tafi yajin aiki.

Sun hori al’umma da cewa, su sani gwamnati ta gaza a alkawuran da suka dauka a tsakaninsu da kungiyar na wajen farfado da jami’o’in kasar nan, hakan yasa suke ganin yasa gwamnatin tarayyar bullo da wannan tsarin biyan albashin na IPPIS domin ta karkatar da hankalin kungiyar a kan yarjejeniyar da suka kulla tun a shekarar 2009.

Daga nan sun bukaci gwamnatin tarayyar da su dauki nauyin da suka dorawa kansu sannan su mutunta tsarin doka wanda ya sabawa hakan zai jefa ilimin jam’o’in ga tabarbarewa, inda suke kan bakarsu ta na ba biyan albashi ba aiki.